Muharram 1446AH: Kungiyoyi Sun Bukaci Tinubu Ya Yi Adalci Ga Al’ummar Musulmai
- Yayin da jihohi ke tabbatar da hutu a ranar 1 ga watan Muharram, kungiyoyin Musulunci sun bukaci sauran jihohi sun yi koyi da su
- Kungiyar Muslim Media Practitioners of Nigeria (MMPN) ta bukaci Gwamnatin Tarayya da sanya 1 ga wata a matsayin ranar hutu
- Kungiyoyin suka ce hakan zai kara tabbatar da cewa ana tafiya tare da Musulmai a harkokin kasar baki daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Wasu kungiyoyin Musulunci sun bukaci Gwamnatin Tarayya ta sanya 1 ga watan Muharram ranar hutu.
Kungiyoyin da suka yi kiran sune Muslim Media Practitioners of Nigeria (MMPN) da Ogun State Muslim Council (OMC).
Muharram: An bukaci Tinubu ya ba da hutu
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kungiyoyin suka fitar ta bakin shugabanninsu, kamar yadda Tribune ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyoyin Musuluncin sun bukaci jihohi da Gwamnatin Tarayya su tabbatar da sanya ranar domin yin hutu a kasar baki daya.
Shugaban kungiyar MMPN, Alhaji Abdur-Rahman Balogun ya ce matakin zai yi dai-dai da tsarin doka ta adalci ga al'ummar Musulmi.
Balogun ya ce hakan zai saka al'ummar Musulmi su ji ana tafiya tare da su a harkokin kasar baki daya, cewar The Guardian.
Kungiyoyin Musulunci sun fadi amfanin hutun
"1 ga watan Muharram kamar 1 ga watan Janairu ne na Turawa, muna bukatar Gwamnatin Tarayya da jihohi su sanya 1 ga watan Muharram ranar hutu."
"Wannan mataki zai tabbatarwa Musulmai cewa ana tafiya tare da su a harkokin da suka shafi kasa baki daya."
- Abdur-Rahman Balogun
Wannan na zuwa ne yayin da wasu jihohi suka sanya 1 ga watan Muharram a matsayin ranar hutu.
Muharram 1446AH: Kano ta ayyana hutu
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin jihar Kano ta sanya 1 ga watan Muharram a matsayin ranar hutu a jihar.
Gwamnatin ta dauki matakin ne domin ba al'ummar Musulmai damar gudanar da addu'o'i a wannan rana mai girma.
Ranar Lahadi 7 ga watan Yulin 2024 za ta kasance ranar 1 ga watan Muharram ta sabuwar shekarar Musulunci.
Asali: Legit.ng