Samoa: Sheikh Yahaya Jingir Ya Bayyana Matsayarsa Kan Yarjejeniyar, Ya Yi Gargadi

Samoa: Sheikh Yahaya Jingir Ya Bayyana Matsayarsa Kan Yarjejeniyar, Ya Yi Gargadi

  • Yayin da ake cece-kuce kan yarjejeniyar Samoa, Sheikh Sani Yahaya Jingir a ya bayyana matsayarsa kan lamarin
  • Sheikh Jingir ya yi fatali da yarjejeniya inda ya ce da Musulmi da Kirista da sauran masu addinai duk sun ce ba za su yi ba
  • Hakan ya biyo bayan sanya hannu a yarjejeniyar Samoa da Gwamnatin Tarayya ta yi da ake zargin ya kunshi auren jinsi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Plateau - Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi tsokaci kan yarjejeniyar Samoa da Gwamnatin Tarayya ta sanyawa hannu.

Shehin malamin ya yi fatali da yarjejeniyar inda ya ce ko kusa ba za a amince da wannan iya shege ba.

Kara karanta wannan

Najeriya za ta samu bashin $150bn da halatta auren jinsi a yarjejeniyar Samoa?

Sheikh Jingir ya yi tsokaci kan yarjejeniyar Samoa a Najeriya
Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi fatali da yarjejeniyar Samoa da aka sanyawa hannu. Hoto: Sheikh Sani Yahaya Jingir.
Asali: Facebook

Samoa: Jingir ya yi fatali da yarjejeniyar

Sheikh Jjngir ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da Abdul'aziz Abubakar ya wallafa a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jingir ya ce da Musulmai da Kiristoci har ma da wadanda ba su da addini ba su amince da hakan ba.

Malamin ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta janye wannan kudiri ba tare da bata lokaci ba saboda ba za su bari ba.

Samoa: Matsayar Jingir kan yarjejeniyar

"Yanzu ga shi wani Minista ya je ya sanya hannu a boye za a ba su biliyoyin dala za a koma luwadi da madigo Allah ya tsare mu."
"Mu ƴan Najeriya Musulmai da Kiristoci har ma wadanda ba Musulmai ba kuma ba Kiristoci ba ba mu yarda ba."
"Waye ne zai shiga gaba ya amince da wannan doka bayan duk ƴan ƙasa ba su yarda ba."

Kara karanta wannan

Samoa: Sheikh Gumi ya yi martani kan yarjejeniyar, ya shawarci gwamnati

"Ku shafe ta mu ba za mu yi luwadi da madigo ba, mu Musulmai mun ce ba za mu yi ba haka Kiristoci ma sun ce ba za su yi ba."

- Sheikh Yahaya Jingir

Tattunawar Legit da wani mabiyin Jingir

Legit Hausa ta tattauna da wani daga cikin mabiya malamin kan martaninsa game da yarjejeniyar Samoa.

Usman Faruk Muhammad ya ce malam ya yi dai-dai kuma dole ne kowane malami ya yi koyi da shi saboda ita gaskiya daya ce.

Faruk ya ce wasu suna sukar malam kan matsayarsa a zabe inda ya ce zabe daban wannan lamari ma daban.

Ya ce duk da korafi da wasu suke yi kan malam amma ya fadi gaskiya kan abin da ke tafiya saboda daman shi domin Allah ya yi.

Samoa: Malamai sun dira kan Bola Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa malaman addinin Musulunci da dama sun yi tsokaci kan yarjejeniyar Samoa da Gwamnatin Tarayya ta sanyawa hannu.

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu: Sheikh Dutsen Tanshi ya dauki zafi kan rigimar Kano, ya fadi matsayarsa

Malaman sun bayyana damuwa kan yarjejeniyar inda suka gargadi gwamnatin kan matsalolin da haka zai haifar a kasa.

Hakan ya biyo bayan sanya hannu a yarjejeniyar wanda Gwamnatin Tarayya ta ce ba shi da alaka da auren jinsi ko kadan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.