Lauya Ta Fayyace Matsayar Yarjejeniyar Samoa Wajen Kawo Auren Jinsi a Najeriya

Lauya Ta Fayyace Matsayar Yarjejeniyar Samoa Wajen Kawo Auren Jinsi a Najeriya

  • Ana ta tsoron cewa za a iya halatta muradun LGBT na dangatakar jinsi saboda Najeriya ta shiga yarjejeniyar Samoa
  • Aysha Hamman wanda kwararriyar lauya ce ta musanya ikirarin, ta ce yarjejeniyar ba za ta iya shafe dokar kasa ba
  • Masaniyar shari’ar ta kawo dalilin da ke nuna yarjejeniyar da aka rattabawa hannu ba ta da ikon kawo wannan al’ada

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Aysha Hamman lauya ce kuma mai gwagwarmya domin kare hakkin marasa karfi, tayi rubutu game da yarjejeniyar Samoa.

Lauyar ta yi wannan bayani ne ganin yadda ake ta surutu, ana zargin gwamnatin tarayya ta kama hanyar halatta dangantakar jinsi.

Samoa
Gwamnatin Bola Tinubu ta sa hannu a yarjejeniyar Samoa Hoto: @Dolusegun
Asali: Twitter

Lauya ta yi karin haske kan Samoa

Kara karanta wannan

Najeriya za ta samu bashin $150bn da halatta auren jinsi a yarjejeniyar Samoa?

A rubutun da Aysha Hamman ta yi a shafin X, ta ce shiga yarjejeniyar bai nufin kawo auren jinsi, hakan ya dace da rahoton the Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masaniyar harkar shari’ar ta ce dalili kuwa shi ne akwai dokar da Dr. Goodluck Jonathan ya rattabawa hannu da yake kan mulki a 2014.

Wannan doka ta na kunshe da hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari ga duk wanda aka samu yana yi ko tallata wata alakar jinsi.

Samoa: Sa hannu zai halatta auren jinsi?

Saboda haka lauyar ta ce shiga yarjejeniyar samoa kadai bai isa ya tunkude abin da ‘yan majalisa su ka kawo a kundin tsarin mulki ba.

Ta ce muddin ba a shafe wannan doka ta haramcin auren jinsi ba, yarjejeniyar samoa ba za ta iya rusa ta ba saboda wasu dalilan shari'a.

Kara karanta wannan

Tallafin N729bn: Ministar Buhari ta shiga matsala, kotu ta karbi korafin SERAP

Abubuwan da za su hana Samoa tasiri

Da farko dai a tsarin mulki akwai karfin ikon yin doka ya rataya ne a kan wuyan majalisa.

Sannan tsarin mulki ya raba aikin da yake kan kowa, bangaren zartarwa ba shi ne yake da ikon yin doka ba, aikinsa shi ne aiwatarwa.

Ko yana so Barista Aysha Hamman ta ce da kamar wuya, majalisar tarayya ta kyale shugaban kasa ya kawo abin da ya ci karo da doka.

Baya ga haka, wata yarjejeniya da aka shiga ba ta kai karfin abin da yake cikin kundin tsarin mulki, gwamnati ta fadi irin haka haka.

Lauya ta rusa tsoron kawo auren jinsi

Wata hujja kuma da lauyar ta kawo shi ne alkawuran da aka dauka a ketare irinsu Samoa ba za su iya warware dokokin cikin gida ba.

Ko kotu aka je, Aysha Hamman ta ce ba za a iya tursasa muradun LGBT a Najeriya ba, lamarin da duk addinan kasar sun soke shi.

Kara karanta wannan

Samoa: Tinubu zai dauki mataki kan Daily Trust game da rahoton yarjejeniyar da aka yi

Majalisar shari'a za ta duba yarjejeniyar Samoa

Rahoton da aka samu shi ne Majalisar kolin shari’ar addinin musulunci za ta bibiyi yarjejeniya da gwamnati ta rattabawa hannu.

Sheikh Bashir Aliyu Umar ya tabbatar da cewa sai sun yi nazarin Samoa sannan za su dauki matsaya tare da jan hankalin hukuma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng