Samoa: Hudubobin Malamai Sun Dura Kan Tinubu Saboda Tsoron Halatta Auren Jinsi

Samoa: Hudubobin Malamai Sun Dura Kan Tinubu Saboda Tsoron Halatta Auren Jinsi

  • A hudubobin Juma’a da aka yi, an ji yadda aka yi inkarin amincewa aure da dangantakar jinsi a Najeriya
  • Malaman addinin musulunci a fadin kasar nan sun nuna ba za su yi na’am da abin da zai kare luwadi da madigo ba
  • Sheikh Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu ya yi magana yayin da jama’a su ka tsorata da yarjejeniyar Samoa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Malaman addinin musulunci da-dama sun fito sun yi magana bayan jin labarin Najeriya ta shiga yarjejeniyar Samoa.

Abin da ya jawo surutu da korafi shi ne ganin cewa akwai batun halatta aure da dangantakar jinsi a wannan yarjejeniya.

Samoa
Shugaba Bola Tinubu ya sa hannu a yarjejeniyar Samoa Hoto: @officialABAT/@DrDennisOuma
Asali: Twitter

Labarin ya karade gari ne bayan wani rahoto da Daily Trust ta fitar a safiyar Alhamis, sai aka yi sa’a an tado batun daf da Juma’a.

Kara karanta wannan

Samoa: Bashir Aliyu Umar ya fadi matakin da majalisar shari’a za ta dauka kan gwamnati

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hudubobi sun tabo yarjejeniyar Samoa

A hudubobin da aka gabatar a garuruwa dabam-dabam, malaman addinin musulunci sun nuna ba za su goyi bayan alakar jinsi ba.

Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu wanda malami ne a jami'a a hudubarsa ta Juma’a ya yi tir da yadda aka amince da yarjejeniyar.

Shehin malamin ya ce bayan an shiga halin wayyo Allah saboda zunuban da ba su kai luwadi ba, ana neman kawo fasadi a kasa.

Malamin musulunci ya misalta lamarin da masifar da ta fi kowace tare da bayanin irin hukuncin addini a kan luwadi da madigo.

Samoa: Sheikh Gadon Kaya ya soki yarjejeniyar

Sheikh Abdallah Usman Gadon Kaya yana cikin wadanda suka yi magana a kan lamarin a mimbarin Juma’a, har ya soki gwamnati.

Gadon Kaya ya ce bai dace a sa hannu a yarjejeniyar ta Samoa ba da amincewar al’umma ba tun ana mulkin damaukaradiyya ne.

Kara karanta wannan

An cafke uban da ya daure dansa mai shekaru 5 cikin sarka ya hana shi abinci

Malami ya yi maganar Samoa a shari'a

A shafin X, Muammar Gaddafi ya daura hudubar Barista Ishaq Adam inda aka ji yana tsokaci game da batun ta fuskar dokar kasa.

Malamin ya tunawa jama’a a kundin tsarin mulki. Najeriya ta na da dokar haramta auren jinsi da ta sha gaban yarjeniyar ta Samao.

"Addinai sun haramta auren jinsi" - Malami

Ana da labari cewa Dr. Bashir Aliyu Umar ya ce musulmai da kirista duk sun yi inkarin auren jinsi a hudubar Juma'ar da ya gagabatar.

Babban malamin ya gargadi hukuma a kan bude kofar halatta luwadi da madigo, ya na mai jan kunne cewa hakan zai kawo masifa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng