“Da Kun Yi Koyi da Magabatanku”: Farfesa Ya Shawarci Aminu Ado da Sanusi II

“Da Kun Yi Koyi da Magabatanku”: Farfesa Ya Shawarci Aminu Ado da Sanusi II

  • Farfesa Umar Labdo ya yi karin haske kan dambarwar sarautar Kano inda ya ba masu rigimar shawara game da shawo kan matsalar
  • Farfesan ya ce tun farko ya kamata Sanusi II da Aminu Ado su yi koyi da Muhammadu Sanusi I bayan tube shi a sarauta
  • Labdo ya ce wannan rigimar cikin gida ne wanda 'yan siyasa ke kara hura wutar domin biyan bukatar kansu a jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Yayin da ake ta dambarwa kan sarautar Kano, Farfesa Umar Labdo ya ba da shawarar kawo karshen rigimar.

Umar Labdo ya ce da a ce Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado sun yi koyi da magabatansu da wannan rigima ba ta taso ba.

Kara karanta wannan

Alkali ya yi barazanar daure Hadimin Gwamna Abba kan shari'ar Ganduje

Farfesa ya nemo hanyar kawo karshen rigimar Aminu Ado da Sanusi II
Farfesa Umar Labdo ya shawarci Aminu Ado da Sanusi II su yi koyi da magabatansu. Hoto: Masarautar Kano, Sanusi Lamido Sanusi.
Asali: Facebook

Sarautar Kano: Farfesa ya koka kan rigimar

Farfesan ya bayyana haka a cikin wata hira da ya yi da jaridar Vanguard inda ya bayyana damuwa kan matsalar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Labdo ya ce ya kamata tun farko sarakunan sun yi koyi kakan Sanusi II wanda ake kira Muhammadu Sanusi I bayan tube shi a Jamhuriya ta daya.

Ya ce gwamnan wancan lokaci, Abubakar Rimi ya yi kokarin dawo da shi sarauta amma yaki amincewa inda ya ce ba zai yi gardama da dan uwansa ba.

"Matsalar cikin gida ne, amma iyalan sun bari 'yan siyasa na amfani da su suna farraka su, hakan abin takaici ne ya kamata su nuna girma."
"Wannan ba shi ne karon farko da ake tube sarki ba, mun ga abin da ya faru da Muhammadu Sanusi I a Jamhuriya ta daya."

Kara karanta wannan

Rigimar sarauta: Farfesa a Kano ya zargi Kwankwaso da saka siyasa tun farkon lamarin

"Gwamnan wancan lokaci, Abubakar Rimi ya yi niyar dawo da Sanusi I amma ya ki inda ya ce ba zai yi rigama da sabon sarkin ba saboda kaninsa ne."

- Farfesa Umar Labdo

Farfesa ya koka kan biris da tarihi

Labdo ya ce da ya kamata sarakunan su yi amfani da wannan tarihi da ya faru wurin dakile rigimar amma sun ki yi.

Ya ce dalilin kin daukar wannan mataki ya jawo duka wannan rigima da ake yi kuma su 'yan Kano suna fushi da hakan.

An zargi Kwankwaso da siyasantar da sarauta

A wani labarin mai kama da wannan, mun kawo muku cewa Farfesa Umar Labdo ya bayyana musabbabin rikicin sarautar Kano.

Farfesan wanda ke koyarwa a Jami'ar Yusuf Maitama Sule da ke jihar Kano ya ce siyasa ce ta jawo wannan rigima tun asali.

Ya ce Rabiu Kwankwaso ya nada Sanusi II saboda ya batawa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan rai bayan ya kore shi daga gwamnan bankin CBN.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Shehu Sani ya magantu da jin an nemi a hana Gwamna Abba fita kasar waje

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.