Muhammadu Sunusi II da kansa ya kira ma kansa ruwa – Farfesa Labdo

Muhammadu Sunusi II da kansa ya kira ma kansa ruwa – Farfesa Labdo

Wani babban malami a fannin tsarin siyasar Musulunci dake jami’ar Yusuf Maitama Sule, Kano, Farfesa Umar Muhammad Labdo ya bayyana cewa tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sunusi ne ya kira ma kansa ruwa har ta yi awon gaba da rawaninsa.

Idan za’a tuna gwamnatin jahar Kano a karkashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje ce ta sanar da tsige Muhammadu Sunusi a ranar Litinin ta hannun sakataren gwamnatin jahar Alhaji Usman Alhaji.

KU KARANTA: Muhammadu Sunusi mai murabus ya koma kauyen Loko a jahar Nassarawa

Muhammadu Sunusi II da kansa ya kira ma kansa ruwa – Farfesa Labdo
Muhammadu Sunusi II da kansa ya kira ma kansa ruwa – Farfesa Labdo
Asali: Facebook

Gwamnatin ta bayar da hujjojinta guda uku wanda ta bayyana su ne suka sabbaba gwamnan daukan mataki mai tsauri a kan Sarkin da suka hada da rashin da’a, kin halartar zaman tattaunawa da kuma karya dokokin masarautar Kano, kamar yadda sakataren gwamnatin jahar Kano ya bayyana.

Sai dai tuni gwamnatin ta sanar da tsohon Sarkin Bichi, Aminu Ado Bayero a matsayin sabon Sarkin Kano, yayin da dan uwansa Nasiru Ado Bayero ya zama sabon Sarkin Bichi.

Labdo ya bayyana haka ne cikin wata ganawa da ya yi da jaridar Daily Trust inda yace tun da Sunusi ya kutsa kansa a cikin al’amuran siyasa, daga nan ya debo ruwan dafa kansa, kuma shi ne sanadiyyar halin da ya shiga a yanzu.

A cewar Farfesan, shiga siyasar da Sunusi ya yi a zaben data gabata ya saba ma al’adun masarauta. “Abin takaici ne yadda yan siyasa ke wasa da masarauta, amma Sunusi shi ya janyo ma kansa, ya cika surutu, sarakan gargajiya na da hanyoyin bayar da gudunmuwa ga tafiyar da mulki, amma ba’a bayyane ba.”

Haka zalika Labdo ya zargi Sunusi da shigo da wasu al’adun turawa cikin masarautar, inda yace: “Ya fi karkata ta bangaren mata, yana sukar maza, ya fada ma mata su rama idan mazajensu sun maresu, wannan ya saba ma al’adunmu a Afirka, yana magana ba tare da la’akari da fahimtar jama’a ba.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel