Aliko Dangote ya Bayyana Tsawon Lokacin Da Za a Dauka Wajen Farfado da Tattalin Arziki

Aliko Dangote ya Bayyana Tsawon Lokacin Da Za a Dauka Wajen Farfado da Tattalin Arziki

  • Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote ya bayyana cewa tattalina arzikin kasar nan zai farfado nan da watanni kadan
  • Ya bayyana haka ne jim kadan bayan shugaban kasa, Bola Tinubu ya rantsar da shi da sauran masu ruwa da tsaki a bangaren kasuwanci
  • An rantsar da su ne a matsayin 'yan majalisa ta musamman da za ta duba hanyoyin da za a bi wajen gyara tattalin arzikin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote ya bayyana tsawon lokacin da za a dauka wajen dawo da tattalin arzikin Najeriya cikin hayyacinsa.

Aliko Dangote na ganin nan da 'yan watanni kadan za a samu nasarar da ake nema na gyara tattalin arziki da a yanzu ke cikin matsala.

Kara karanta wannan

Dangote, Elumelu sun samu shiga yayin da Tinubu ya rantsar da kwamitin tattalin arziki

Aliko
Aliko Dangote ya ce za a farfado da tattalin arzikin kasa cikin watanni kadan Hoto: Bloomberg
Asali: Getty Images

Daily Trust ta tattaro cewa Dangote ya bayyana haka ne a zantawarsa da 'yan jaridar fadar shugaban kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi hakan ne jim kadan bayan shugaba Tinubu ya kaddamar da majalisa ta musamman kan gyara tattalin arziki (PECC).

Dangote ya fadi hanyar gyara tattalin arziki

Shahararren attajirin dan kasuwar, Aliko Dangote ya bayyana cewa hadin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu zai gyara tattalin arzikin kasa.

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa bangarori masu zaman kansu za su bayar da shawarwarin kan manufofin da za su warware matsalolin da ake fuskanta.

Mashahurin dan kasuwar ya yi alkawarin cewa za a samu sauyi mai kyau a kasar nan cikin watanni kadan masu zuwa.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ne ya kaddamar da majalisar jim kadan bayan bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta sanya N2trn cikin harkar farfado da tattalin arzikin kasa.

Kara karanta wannan

Majalisa ta hango matsala, Sanatoci sun koka kan shigo da gurbataccen mai a Najeriya

Dangote ya zama 'dan majalisar tattalin arziki

A wani labarin kun ji cewa shahararren dan kasuwa, Aliko Dangote ya zama daya daga cikin 'yan majalisa ta musamman kan farfado da tattalin arziki.

A ranar Alhamis ne shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da kwamitin a Abuja, inda ya kunshi 'yan kasuwa, jami'an gwamnati da mashawarta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.