Majalisa Za Ta Binciki Kwangilar Aikin Mambila, Za a Dauko Aikin Wutar Tun Daga 1999

Majalisa Za Ta Binciki Kwangilar Aikin Mambila, Za a Dauko Aikin Wutar Tun Daga 1999

  • Majalisar dattawan Najeriya ta dawo da magana kan wutar Mambila da aka kashe makudan kudi domin samar da ita a shekarun baya
  • A zaman majalisar na jiya Alhamis ne suka tattauna kan yadda za a cigaba da aikin da kuma binciken yadda kuɗin aikin ya salwanta
  • Sanata Muhammadu Danjuma Goje ya tura sako na musamman ga Bola Tinubu kan wutar a yayin zaman majalisar na jiya Alhamis

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta dauki sabon mataki kan aikin wutar Mambila da aka warewa makudan kudi.

A lokacin mulkin Muhammadu Buhari aka yi tsammanin fara amfanuwa da wutar amma sai aikin ya gagara samuwa.

Kara karanta wannan

Majalisa ta amince a kirkiro hukumar cigaban jihohin Arewa, za a jira Tinubu ya sa hannu

Majalisa
Za a yi bincike kan wutar Mambila. Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa majalisar ta tattauna kan lamarin ne a zamanta na jiya Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a yi binciken aikin wutar Mambila

Majalisa ta umurci kwamiti mai lura da harkar makamashi da kudi ya fara bincike kan yadda aka kashe kudi a aikin wutar Mambila ba tare da samar da lantarki ba.

Rahoto ya nuna cewa binciken majalisar zai fara ne tun daga shekarar 1999 har zuwa lokacin mulkin Muhammadu Buhari.

Sanatan da ya dauko maganar wutar Mambila

Sanata Manu Haruna daga Taraba ta tsakiya ne ya jawo hankalin majalisar kan aikin wutar, rahoton Business Day.

Daga baya kudurin ya samu goyon bayan Sanata Danjuma Goje, Ahmed Lawan da wasu Sanatoci su 26.

Goje: 'Ina goyon bayan aikin wutar Mambila'

Sanata Danjuma Goje ya ce zai ba da dukkan goyon bayan da ake buƙata domin tabbatar da cewa an yi aikin wutar Mambila.

Kara karanta wannan

Dangote, Elumelu sun samu shiga yayin da Tinubu ya rantsar da kwamitin tattalin arziki

Goje ya yi kira ga Bola Tinubu kan saka aikin wutar Mambila cikin manyan ayyukan da gwamnatinsa za ta yi.

Tun a shekarar 2017 gwamantin Najeriya ta ba kamfanin kasar Sin kwangilar aikin a kan $5.92bn amma aikin ba yiwu ba har yau.

An sace randar lantarki a Gombe

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Gombe karkashin jagorancin Muhammadu Inuwa Yahaya ta dauki mataki kan kansila da dagaci bisa zargin sata.

Ana zargin kansilan da dagacin da hada baki wajen sace randar wutar lantarki a Garin Majidadi da ke ƙaramar hukumar Akko.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng