Jerin Makamai da Kwastam Ta Kama Ana Shirin Shigowa da Su Najeriya Cikin Shekaru 7

Jerin Makamai da Kwastam Ta Kama Ana Shirin Shigowa da Su Najeriya Cikin Shekaru 7

  • Shekaru da dama hukumar kwastam na kama makamai masu dimbin yawa da ake kokarin shigowa da su tarayyar Najeriya
  • Sai dai masu sharhi suna ganin rashin yin hukunci mai tsauri ga waɗanda ke shigowa da makaman ne ya sa lamarin yaki karewa
  • A wannan rahoton, Legit ta yi waiwaye cikin shekarun baya domin bayyana muku irin makamai da hukumar kwastam ta kama

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Hukumar kwastam ta shahara da kama makamai da ake kokarin shigowa da su Najeriya.

Ko cikin makon nan hukumar ta sanar da kama dimbin makamai da ake ƙoƙarin shigowa da su Najeriya daga Turkiyya.

Hukumar Kwastam
An kama makamai da dama daga 2017 zuwa yau. Hoto: Nigeria Customs Service
Asali: Facebook

Legit za ta tattaro muku lokutan da hukumar ta kama makamai da ake kokarin shigowa da su Najeriya a shekarun baya.

Kara karanta wannan

Yan sandan Kano sun cafke 'yan bindiga da 'yan daba sama da 100 cikin kwanaki 10

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babu mamaki an yi kame-kame da yawa, amma wadannan sun fi jan hankali sosai.

2017: Kwastam ta kama makamai a Legas

A watan Janairun shekarar 2017, hukumar kwastam ta kama makamai masu tarin yawa a jihar Legas.

Makaman sun hada da bindigogi guda 661 da aka boye cikin manyan akwati guda 49, rahoton Channels Television.

Bincike ya nuna cewa an kera bindigogin ne daga kasar Sin aka biyo da su ta Turkiyya domin shigo da su Najeriya.

2021: Kwastam ta kama makamai a Legas

A watan Disambar shekarar 2021 hukumar kwastam ta kama makamai masu yawa ana ƙoƙarin shigowa da su Najeriya.

Mutumin da aka kama da kayan ya yi ikirarin cewa talabijin ya dauko amma bayan an yi bincike sai aka gano bindigogi ne, rahoton the Cable.

2023: Kwastam ta kama makamai a Legas

Kara karanta wannan

Komai ya tsaya cak, mamakon ruwan sama ya wanke unguwanni a Legas

A watan Yulin shekarar 2023 hukumar kwastam ta kama nau'in makamai har guda 10 a Legas ciki har da bindigogi da dama.

Hukumar ta tabbatar da cewa a cikin makaman a akwai harsashi jigida 442 kuma ta kama mutane biyu.

2024: Kwastam ta kama makamai a Rivers

Kamar shekarun baya, hukumar kwastam ta kama makamai ana ƙoƙarin shigowa da su Najeriya a cikin makon nan a jihar Rivers.

Shugaban hukumar, Bashir Adeniyi ya ce sun kama bindigogi guda 844 da harsashi guda 112,500 a wannan karon.

Sai dai duk da kamun da hukumar ke yi ana hasashen akwai miyagun da suke wucewa ba a gane su ba kuma ba a ji hukumar na bayyana irin hukuncin da ake yankewa waɗanda ake kamawa ba.

Kwastam ta kama masu safarar mai

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar kwastam ta Najeriya ta yi bayani bayan mako biyu da ta shafe tana samame kan masu safarar man fetur zuwa ketare.

Kara karanta wannan

NSCDC ta kama ɗan damfara da ya karbi N4.5m domin samar da kujerun Hajji

Hukumar ta yi samamen ne kan iyakokin Najeriya ta sassa daban-daban domin gano barnar da ake tafkawa kan safarar mai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng