Hukumar Kwastam ta kama manyan bindigogi sama da 200,000 a jihar Neja

Hukumar Kwastam ta kama manyan bindigogi sama da 200,000 a jihar Neja

Hukumar fasakwabri na kasa Kwastam ta kama wata babban mota dauke da muggan makamai 200,000 da aka shigo dashi ta barauniyar hanya daga jamhuriyar Benin.

Jami'an hukumar da ke sintiri a Babana, wani kauye dake kan iyakar jihar Neja da jamhuriyar Benin ne suka kama motar kuma suka gano cewa an boye makaman ne a wata kusurwa ta karya da aka yi a karkashin motar.

An kama direban motar da wani mutum da ke tare dashi a motar wanda ya ce sunansa Martin Anokwara.

Kwastam ta kama babban mota dauke da bindigogi fiye da 200,000 a jihar Neja
Kwastam ta kama babban mota dauke da bindigogi fiye da 200,000 a jihar Neja

DUBA WANNAN: Da Azikiwe yana raye tabbas zai goyawa Buhari baya

A cewar Mr Anokwara, ya ciyo bashin makaman ne daga hannun wani dilali a Cotonou saboda ya sayarwa mafarauta a garin Onitsha na jihar Anambra.

Kwantrolla na kwastam mai kula da jihohin Neja, Kwara da Kogi, Mr Benjamin Binga ya yabawa kokarin jami'an da su kayi wannan kamun.

Ya kuma shawarci masu irin wannnan mummunar sana'a su dena su nemi wani hanyar cin abinci na hallas. Ya kuma yi kira da mutane su cigaba da bawa hukumar hadin kai wajen gannin ta cigaba da gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.

A wata rahoton, Legit.ng ta kawo muku labarin yadda Sojin Najeriya ta saki kananan yara 138 wanda Boko Haram ta rika amfani dasu wajen yaki.

A jawabinsa wajen taron mika yaran da akayi a jiya a Maiduguri, Shugaban hafsin sojin kasa na Najeriya, Laftanat Janar Tukur Buratai ya ce yaran da aka saki sun hada da mata takwas da maza guda 175.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164