'Yan Kwangilar Gwamnati 39 Sun Shiga Matsala, Majalisa Za Ta Gurfanar da su

'Yan Kwangilar Gwamnati 39 Sun Shiga Matsala, Majalisa Za Ta Gurfanar da su

  • Majalisar dattawa ta shirya gurfanar da 'yan kwangila 39 da suka ƙi fara ayyukansu bayan karɓar kuɗi daga gwamnatin tarayya
  • Ministan ayyuka, David Umahi, ya ce za su yi amfani da hukumar EFCC wurin karɓo kudinsu daga wadannan 'yan kwangilar
  • Sanata Umahi ya sanar da zunzurutun ayyukan da ba a fara ba kuma ya tabbatar da za a ƙwace kwangilar kacokan daga hannunsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kwara - Aƙalla 'yan kwangila 39 ne da aka baiwa kwangila suka gaza fara aiki, kamar yadda shugaban kwamitin ayyuka na majalisar dattawa, Sanata Barinada Mpidi ya bayyana a Ilorin.

Hakazalika, ministan ayyuka, David Umahi ya yi barazanar amfani da hukumar EFCC domin karɓo kudade daga 'yan kwangila 18 wadanda suka gagara fara ayyuka 260.

Kara karanta wannan

Shinkafi ya fadi abin da ke kawo rashin tsaro a Arewa maso Yamma, ya ba da mafita

Majalisa za ta gurfanar 'yan kwangila 39 da suka ki aiki. Hoto daga The Nigerian Senate
Majalisar Dattijai Za Ta Gurfanar Da 'Yan Kwangila 39 Da Suka Kalmashe Kudin Gwamnati
Asali: Facebook

Majalisa za ta gurfanar da 'yan kwangila

Sanatan da kuma ministan sun sanar da hakan ne a jihar Kwara, yayin tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan aikin babbar hanyar Sokoto zuwa Badagry, inji rahoton jaridar Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Barinada Mpigi, wanda ya sanar da masu ruwa da tsaki cewa aƙalla 'yan kwagila 39 da gwamnatin tarayya ta ba aiki sun kasa farawa, ya ce majalisar za ta gurfanar da su.

Ya ƙara da cewa:

"Majalisa ta fusata da abinda 'yan kwangilar suka yi. Muna kira ga ministan ayyuka da ya datse ayyukan 'yan kwangilar da ba su fara aiki ba."

- Barinada Mpigi

Kwangila: Gwamnati za ta yi amfani da EFCC

Jaridar Vanguard ta ruwaito ministan ayyuka, Sanata David Umahi ya ce 'yan kwangila 18 masu ayyuka 260 sun ƙi zuwa su fara aiki.

Kara karanta wannan

Borno: Majalisar dattawa ta faɗi sakacin da ya jawo aka kai harin bam a Gwoza

"Za mu ƙwace kwangilar duk wani ɗan kwangilar da ya karbi kudin fara aiki amma ya ƙi farawa. Za mu yi amfani da hukumar EFCC wurin karɓo kudinmu."

- David Umahi.

Ministan ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya tana da ayyuka 18 a Kwara, inda ya ƙara da cewa 10 daga ciki basu fara aikin ba.

Ɗan majalisa ya fusata da Ben Kalu

A wani labari na daban, mun ruwaito cewa Hon. Cyril Hart dan majalisar wakilai daga mazaɓar Bonny/Degema a jihar Ribas ya fusata da mataimakin kakkin majalisa, Ben Kalu.

Hon. Cyril Hart ya zargi Ben Kalu, da ware sababbin zuwa majalisar yayin tattaunawa a zauren, inda daga bisani ya fusata da kamalam mataimakin kakakin, ya fice daga zauren majalisar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.