Rikicin Sarauta: Kotu Ta Ba Lauyoyi Sabon Umarni a Shari'ar Masarautun Kano
- Babbar kotun jihar da ke sauraron ƙara kan rikicin masarautun Kano ta hana lauyoyin da ke cikin shari'ar yin hira da ƴan jarida
- Alƙaliyar kotun, mai shari'a Amina Adamu Aliyu ita ce ta umarci lauyoyin da kada su yi hira da ƴan jarida kafin ko bayan hukuncin da za ta yanke
- Mai shari'ar ta bayar da umarnin ne a yayin zaman kotun a birnin Kano na ranar Alhamis, 4 ga watan Yulin 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Mai shari’a Amina Adamu Aliyu ta babbar kotun jihar Kano da ke zamanta a sakatariyar Audu Bako, Kano, ta ba lauyoyin da ake shari'ar masaurautun Kano da su sabon umarni.
Mai shari'a Amina Adamu Aliyu ta umarci lauyoyin da su daina yin hira da manema labarai.
Wane umarni alƙaliyar ta ba da?
Alƙaliyar kotun ya bayar da umarnin ne a lokacin da ake ci gaba da shari’ar, a ranar Alhamis, 4 ga watan Yulin 2024, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Umarni na ne a gare ku (lauyoyi) da ka da ku yi hira da ƴan jarida kafin ko bayan na yanke hukunci kan roƙon da wanda ake ƙara na farko ya gabatar na neman daina wannan shari'ar."
- Amina Adamu Aliyu
Jim kaɗan bayan bayar da wannan umarnin, sai mai shari'ar ta tafi hutun taƙaitaccen lokaci kafin ta dawo ta yanke hukunci kan ƙarar da ke gabanta ta dambarwar masarautun, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.
Batun shari'ar masarautun Kano
Waɗanda suka shigar da ƙarar sun hada da Antoni Janar na Kano, kakakin majalisar dokokin jihar Kano da majalisar dokokin jihar Kano, ta hannun lauyansu Ibrahim Isah-Wangida, Esq.
Sun shigar da ƙarar ne a ranar 27 ga watan Mayun 2024 inda suka buƙaci kotun ta hana Aminu Ado-Bayero da sarakunan Bichi, Rano, Gaya da Karaye da aka rushe masarautunsu daga ayyana kansu matsayin sarakuna.
Waɗanda ake ƙarar sun haɗa da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado-Bayero, Sarkin Bichi, Nasiru Ado-Bayero, Sarkin Karaye, Dr Ibrahim Abubakar ll, Sarkin Rano, Alhaji Kabiru Muhammad-Inuwa da Sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim-Gaya.
Sauran sun haɗa da Sufeto Janar na ƴan sandan Najeriya, daraktan dukumar DSS na Kano, kwamandan sibil difens na Kano da rundunar sojojin Najeriya.
Kotu ta ɗage sauraron shari'a
A wani labarin kuma, kun ji cewa babbar kotun jihar Kano ta ɗage zaman sauraron shari'ar da ke gabanta kan rushe masarautu biyar da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, ya ƙirƙiro.
A ƙarar an roƙi babbar kotun jihar ta haramtawa Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna huɗu ayyana kansu a matsayin halastattun sarakuna.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng