An Mikawa Gwamnatin Zamfara 'Yan Mata da Samarin da Aka Ceto a Hannun 'Yan Bindiga

An Mikawa Gwamnatin Zamfara 'Yan Mata da Samarin da Aka Ceto a Hannun 'Yan Bindiga

  • Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya mika mutanen da aka sace a jihar Zamfara ga gwamnati
  • A yau Alhamis ne aka mika mutanen a ofishin da ke kula da yaki da ta'addanci karkashin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro
  • An sace mutanen ne a yankunan Zurmi, Duran, da Gusau tun ranar 22 ga watan Afrilu wanda ya dauki lokaci kafin jami'an tsaron su ceto su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta mika mutanen da aka sace a jihar Zamfara ga jami'an gwamantin jihar.

A yau Alhamis ne aka mika mutanen bayan an ceto su daga hannun yan bindiga a ranar 27 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Matashin da ya hallaka masallata a Kano ya amsa laifinsa, Kotu ta fitar da matsaya

Nuhu Ribadu
An mika mutanen da aka sace ga gwamnatin Zamfara. Hoto: Nuhu RIbadu.
Asali: Facebook

Jaridar the Guardian ta ruwaito cewa manyan jami'an gwamnatin jihar Zamfara ne suka karbe su a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adadin mutanen Zamfara da aka ceto

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya mika matane 16 da ake ceto daga hannun masu garkuwa da mutane.

An ceto mutanen wadanda suka hada da maza takwas da mata takwas ne a ƙananan hukumomin Tsafe da Shinkafi.

Gwamnati za ta kara kokari kan tsaro

A yayin mika mutanen, gwamantin tarayya ta ce za ta cigaba da ƙoƙarin yaki da masu garkuwa da mutane a Najeriya.

Saboda haka ta bukaci yan Najeriya da su rika sanar da jami'an tsaro duk wani motsi da ba su yarda da shi ba.

Waɗanda suka karbi mutanen

Sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Alhaji Abubakar Nakwada ne ya jagoranci karbar mutanen a Abuja, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Borno: Majalisar dattawa ta faɗi sakacin da ya jawo aka kai harin bam a Gwoza

A cikin tawagar har ila yau akwai kwamishinan zartar da ayyuka na jihar Zamfara, Alhaji Zurumi Nasiru.

An kai hari jihar Zamfara

A wani rahoton, kun ji cewa yan bindiga sun kai wasu sababbin hare-haren ta'addanci a Zamfara wacce ta daɗe tana fama da matsalar rashin tsaro.

Miyagun ƴan bindigan sun hallaka mutum takwas a wani sabon hari da suka kai a garin Faru da ke ƙaramar hukumar Maradun ta jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel