Akwai Bindigogi Sama da 277 Kewaye da Zauren Majalisa, Sanatan APC Ya Fallasa
- Sanata Jimoh Ibrahim ya ce wata manhaja da ke cikin wayarsa ta gano bindigogi sama da 277 a zauren majalisar dattawa
- Sanatan mai wakiltar Ondo ta Kudu ya ce akwai bukatar jami'an tsaron Najeriya su koma amfani da fasaha wajen yaki da rashin tsaro
- Sanata Jimoh ya kuma ce bindigogi 277 da wayarsa ta gano ba zai rasa kusancin majalisar da dakin ajiyar makamai na Aso Rock ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Sanata mai wakiltar Ondo ta Kudu, Jimoh Ibrahim, ya ce yana da manhaja a wayarsa da ke gano adadin bindigogin da ke kusa da shi a kowane lokaci da kuma duk inda ya je.
Sanata Jimoh Ibrahim ya bayyana bukatar amfani da fasaha wajen yaki da rashin tsaro, inda ya ce wayarsa ta gano bindigogi sama da 277 a zauren majalisar dattawa.
Wayar sanata ta gano bindigogi a majalisa
Sanatan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin tsokaci kan kudirin da Sanata Ali Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu ya gabatar, in ji rahoton The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kudurin da Sanata Ndume ya gabatar na magana ne kan harin kunar bakin wake da aka kai a Gwoza, karamar hukumar da ke karkashin mazabarsa ta majalisar dattawa.
Sanata Jimoh ya ce bai firgita da yawan bindigogin da ke kewaye da shi ba, domin ya san majalisar dokokin kasar tana kusa da dakin ajiye makamai na Aso Rock.
"Sai mun tashi tsaye" - Sanata Jimoh
Rahoton Channels TV ya yi nuni da cewa Sanata Jimoh ya ce sai Najeriya ta tashi tsaye wajen yaki da ta'addancin inda ya nemi sojoji da su karfafa yin amfani da fasahohin zamani.
“Abin da nake nufi a nan shi ne, akwai bukatar mu koma yin amfani da fasaha wajen yaki da 'yan ta'adda maimakon amfani da sojojinmu kamar yadda Sanata Ndume ya ce.
“Yayin da nake tsaye a nan, na kan duba wayata akai-akai kuma na san adadin bindigogin da ke kusa da ni. Akwai sama da bindigogi 277 yanzu haka."
Majalisa ta magantu kan harin Borno
A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar wakilan Najeriya ta ce za ta bincike musabbabin abin da ya jawo tashin bam din kunar bakin wake a Gwoza, jihar Borno.
Dan majalisa mai wakiltar mazabar Damboa/Gwoza/Chibok a jihar Borno, Hon. Ahmad Jaha ya ce akwai sakacin jami'an tsaro da mutanen yankin kan tashim bam din.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng