'Yan sanda sun gano bindigogi 107 a jihar Anambra

'Yan sanda sun gano bindigogi 107 a jihar Anambra

- ‘Yan Sanda sun gano bindigogi 107 da harsasai daga hannun wadanda doka bata basu izinin amfani dasu ba a jihar Anambara

- IGP Idris ya bayarda da umurnin cewa duk wasu makamai da ake amfani dasu a kasar nan ba da izinin doka ba a karbesu

- Kwamishinan ‘Yan Sanda Garba Umar na jihar Anambara yace wasu daga cikin wadannan makamai an samesu daga hannun masu amfani dasu cikin lalama

‘Yan Sanda sun gano bindigogi 107 da harsasai daga hannun wadanda doka bata basu izinin amfani dasu ba a jihar Anambara. Sifeta Janar Idris ya bayarda da umurnin cewa duk wasu makamai da ake amfani dasu a kasar nan ba da izinin doka ba a karbesu.

'Yan sanda sun gano bindigogi 107 a jihar Anambra
'Yan sanda sun gano bindigogi 107 a jihar Anambra

Kwamishinan ‘Yan Sanda Garba Umar na jihar Anambara yace wasu daga cikin wadannan makamai an samesu daga hannun masu amfani dasu cikin lalama.

DUBA WANNAN: Shugabanin addinin kiritsa sunki amincewa da tazarcen Buhari

Jaridar Vanguard sun ruwaito cewa kwamishinan ‘Yan Sanda Garba Umar, wanda ya gabatar da makaman a Helikwatar Ofishinsu dake Awka, a ranar Alhamis 5 ga watan Afirilu, yace anyi hakan ne bisa ga umurnin shuagaban hukumar ta ‘Yan Sandan Najeriya.

Legit.ng ta ruwaito cewa a jihar Sokoto hukumar ‘Yan Sandan ta gano makamai 948 a watanni 24 da suka gabata. Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Murtala Mani ya bayyana haka a ranar Laraba 24 ga watan Afirilu a wurin taron da suka gabatar a jihar Sokoto.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164