Sheikh Dahiru Bauchi Sun Rabu da Sanusi II, An Shirya Zikiri a Fadar Aminu Ado Bayero

Sheikh Dahiru Bauchi Sun Rabu da Sanusi II, An Shirya Zikiri a Fadar Aminu Ado Bayero

  • Gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi tana farin cikin gayyatar ƴan uwa Musulmai zuwa taron zikirin Juma'a na shekara a jihar Kano
  • Za a gudanar da taron ne a gobe Juma'a 5 ga watan Yulin 2024 a fadar Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero da ke fadar Nassarawa
  • Wannan na kunshe ne a cikin sanarwa da Sayyadi Ibrahim Dahiru Bauchi ya fitar inda ya ce za a yi taron da misalin karfe 4.00 na yamma

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Yayin da ake ci gaba da dambarwa kan sarautar Kano, Sheikh Dahiru Bauchi zai gudanar da zakiri a fadar Nassarawa.

Gidauniyar Shehin malamin za ta gudanar da taronta na zikirin Juma’a na shekara a fadar Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero.

Kara karanta wannan

Jihohin Arewa 3 da aka samu sabani tsakanin sababbin gwamnoni da sarakunan gargajiya

Dahiru Bauchi zai gudanar da zikiri a fadar Aminu Ado
Gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi za ta gudanar da zikiri a fadar Aminu Ado Bayero. Hoto: Masarautar Kano, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Asali: Facebook

Za a yi zikiri a fadar Nassarawa

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sayyadi Ibrahim Dahiru Bauchi ya sanyawa hannu da Masarautar Kano ta wallafa a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a gudanar da zikirin ne kamar yadda aka tabbatar a gobe Juma’a 5 ga Yulin 2024 a fadar da misalin karfe 4.00 na yamma.

Sheikh Dahiru Bauchi shi ne zai kasance babban baƙo na musamman a wurin taron wanda kuma shi ne ya shirya zikirin.

Kano: Tinubu ne babban bako a taron

Ana sa ran manyan bakin da za su halarci zikirin sun hada da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero da Shugaba Bola Tinubu.

Har Ila yau, a yayin taron za a gudanar da addu'o'i na musamman domin shawo kan matsalolin da ƙasar ke fuskanta a bangarori da dama.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta mayar da martani kan ɗaga tuta a fadar da Aminu Ado ke zaune

Iyalan Dahiru Bauchi sun ziyarci Sanusi II

A wani labarin mai kama da wannan, mun kawo muku cewa iyalan Sheikh Dahiru Bauchi sun ziyarci Muhammadu Sanusi II a fadarsa.

Tawagar ta kai ziyarar karkashin jagorancin ɗansa mai suna Aminu Dahiru Bauchi domin yin mubaya'a da nuna goyon baya.

Hakan ya biyo bayan ci gaba da dambarwa da ake yi kan sarautar Kano tsakanin Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel