Ambaliyar Ruwa: Gwamnati Ta Fadi Jihohi da Za Su Fuskanci Barazana Sosai
- Yayin da damuna ke kara kankama, gwamnatin tarayya ta ambaci jihohin da za su fuskanci barazanar ambaliyar ruwa sosai
- Gwamnatin tarayya ta ambaci lokacin da ambaliyar ruwa zai yi ƙamari saboda al'ummar Najeriya su shirya dabarun kare kai
- Ministan ruwa da tsaftar muhalli, Farfesa Joseph Utsev ne ya bayyana lamarin ga manema labarai a yau Alhamis, 4 ga watan Yuli
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Nigeria - Yayin da damunar bana ta kankama, gwamantin tarayya ta yi gargadi kan ambaliyar ruwa.
Gwamnatin tarayya ta fadi jihohi 19 inda ake hasashen za a samu ambaliyar ruwa mai muni a Najeriya.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ministan ruwa da tsaftar muhalli, Farfesa Joseph Utsev ne ya bayyana haka a yau Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yaushe za a samu ambaliyar ruwa?
Farfesa Joseph Utsev ya bayyana cewa a karshen watan Yuli da muke ciki za a samu ambaliyar ruwa a jihohi da dama.
Ministan ya ce ambaliyar ruwan na zuwa ne saboda mamakon ruwa da za a rika yi a kwanakin da kuma toshe magudanar ruwa da mutane ke yi.
Jihohin da za a samu ambaliyar ruwa
Ministan ruwa ya lissafa jihohin da za a samu barazanar ambaliyar ruwa sosai a bana. Jihohin su ne:
- Akwa Ibom
- Anambra
- Benue
- Bayelsa
- Cross River
- Delta
- Edo
- Jigawa
- Kogi
- Kebbi
- Kaduna
- Niger
- Nasarawa
- Ondo
- Ogun
- Rivers
- Taraba
- FCT
Ambaliyar ruwa: A kula da kwalara
Ministan ya bayyana cewa ana tsoron ambaliyar ruwa da za samu zai kara ta'azzara cutar kwalara da ake fama da ita a Najeriya, rahoton Radio Nigeria.
Saboda haka ya ce bayan kokarin da gwamnatin tarayya ke yi ya kamata jihohi da kananan hukumomin su kara kokari wajen daukan matakin kariya.
An yi ambaliyar ruwa a Libiya
A wani rahoton, kun ji cewa ambaliyar ruwa mai tsananin ƙarfi ta yi sanadiyyar ɓacewar mutane aƙalla 10,000 a gabashin ƙasar Libya.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin dai ya faru ne a sakamakon wata iska mai ƙarfi da ta hankaɗo ruwan teku cikin biranen yankin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng