Matashin Da Ya Hallaka Masallata a Kano Ya Amsa Laifinsa, Kotu Ta Fitar da Matsaya

Matashin Da Ya Hallaka Masallata a Kano Ya Amsa Laifinsa, Kotu Ta Fitar da Matsaya

  • A yau ne babbar kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a Kano ta ci gaba da sauraron shari'ar matashi Shafi'u Abubakar Gadan
  • Ana zargin shi da watsawa masallata fetur, sannan ya cinna masu wuta inda zuwa yanzu mutane 23 suka kwanta dama
  • Shafi’u Abubakar Gadan ya amsa tuhume-tuhumen kisan ganganci da jiwa jama'a mugayen raunuka, alkali ya dage shari'ar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano- A yau ne babbar Kotun Musulunci da ke zamanta a Rijiyar Zaki ta ci gaba da sauraron shari'ar da ya kashe mutane 23 a karamar hukumar Gezawa a Kano.

Ana zargin Shafi’u Abubakar Gadan da cinnawa masallata wuta bayan ya watsa masu fetur a masallacin da ke garin Gadan, Larabar Abasawa a Kano.

Kara karanta wannan

Tsaro: Sabon kwamishinan 'yan sandan Kano ya umarci sintirin jami'ai babu kakkautawa

Kano map
Matashi Shafi'u ya amsa laifin kisa Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Aminiya ta wallafa cewa matashin ya amsa laifinsa bayan an karanto kunshin tuhume-tuhumen da aka yi masa na kisan ganganci da jiwa jama'a mugayen raunuka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An dage shari'ar kisan masallata a Kano

A shari'ar kisan masallata a Kano, lauyan gwamnati, Barista Salisu Tahir ya nemi kotu ta sahale masu a sanya sunayen dukkanin mutane 23 da suka rasu.

Barista Salisu Tahir ya bayyana cewa sanya sunayen musulmin da aka salwantar da rayuwarsu a kundin tuhumar zai yi dai-dai da laifin da ake tuhumar Shafi'u da su.

“La’akari da cewa yawan wadanda suka mutu sanadiyyar sanya wutar ya karu, muke rokon kotu ta ba mu wata rana don gabatar da sabon caji don mu sanya adadin yawan mutanen da suka mutu sannan mu gabatar da shaidunmu a gaban kotu.”

- Barista Salisu Tahir

Kara karanta wannan

An shiga jimamin mutuwar wata Farfesa cikin wani yanayi maras dadi a gidanta a Maiduguri

Mai Shari’a Halhalatul Huza’i Zakariyya ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 18 da 19 Yuli, 2024 domin fara sauraron shaidu.

Matashi ya fadi dalilin kashe masallata

A wani labarin kun ji cewa matashi Shafi’u Abubakar Gadan ya bayyana dalilin da ya sanya shi kona masallata a garinsu na Gadan.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce matashin na zargin an cuce shi a rabon gado.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel