Sanata Goje Ya Bayyana Yadda Tinubu Ya Manta da Jihohin Arewa 6 a Ayyukan Tituna
- Sanata Muhammadu Danjuma Goje ya koka kan yadda gwamnatin tarayya ta ware wasu jihohin Arewa cikin ayyukan ta da dauko
- Danjuma Goje ya yi magana ne kan yadda gwamnatin tarayya ta ke ƙoƙarin fara manyan ayyukan titi a wasu yankunan Najeriya
- Wasu daga cikin Sanatoci kasar sun bayyana matsayar su kan maganar da Goje ya yi kuma majalisar dattawa ta karbi korafinsu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Arewa - Sanata mai wakiltar Gombe ta tsakiya, Muhammadu Danjuma Goje ya bukaci a sanya Arewa maso gabas cikin ayyukan Bola Tinubu.
Bola Tinubu ya dauki aniyar fara manyan tituna a wasu yankunan Najeriya amma an a zargin an ware jihohin Arewa maso gabas cikin aikin.
Legit ta tattaro bayanan ne cikin wani bidiyo da mai taimakawa Sanata Goje kan harkokin sadarwa, Muhammad Adamu Yayari ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Korafin Sanata Goje kan ayyukan Tinubu
Sanata Danjuma Goje ya bukaci gwamnatin tarayya ta karkato da ayyukan hanya da aka fara a yankunan Kudu da Arewa ta tsakiya zuwa Arewa maso gabas.
Goje ya ce ana ƙoƙarin fara titin Sokoto zuwa Badagry, Legas zuwa Kalaba, Kalaba zuwa Ebonyi, Benue zuwa Abuja amma an bar yankin Arewa maso gabas a baya.
Amfani yin titi a Arewa maso gabas
Sanata Danjuma Goje ya bayyana cewa gaza magance matsalolin tsaro gaba daya a yankin yana da alaka da rashin wadatattun hanyoyi.
Goje ya kuma kara da cewa yin hanya a yankin zai kara haɓaka tattalin Najeriya domin sai an yi hanya kafin samun albarkatun yankin yadda ya kamata.
Majalisa ta karbi korafin Sanata Goje
Sanata Diket Plang daga jihar Filato ya goyi bayan kudirin ta Danjuma Goje ya gabatar a gaban majalisar, rahoton Punch.
A karshe, shugaban majalisa Sanata Godswill Akpabio ya karbi korafin Danjuma Goje inda ya ce fa'idar yin titi a Arewa maso gabas a bayyane ta ke.
An koka kan titi a Arewa maso gabas
A wani rahoton, kun ji cewa gwamonin Arewa maso Gabas sun koka kan yadda rashin tituna masu kyau ke zama barazana ga zaman lafiya a yankin.
Har ila yau, gwamnonin sun kuma bayyana matsalar gurbacewar muhalli daga cikin matsalolin da jihohin Arewa maso Gabas ke fuskanta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng