An Kai Harin Kunar Bakin Wake a Hanyar Kaduna Zuwa Abuja? Gaskiya Ta Bayyana

An Kai Harin Kunar Bakin Wake a Hanyar Kaduna Zuwa Abuja? Gaskiya Ta Bayyana

  • Gwamnatin jihar Kaduna ta musanta rahotannin da aka yaɗa kan cewa an kai harin ƙunar baƙin wake a hanyar Kaduna zuwa Abuja
  • Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar a cikin wata sanarwa sa ya fitar a ranar Laraba ya ce babu ƙamshin gaskiya a rahotannin
  • Kwamishinan ya bayyana cewa jami'an tsaron da ke kan hanyar su na sanar da gwamnati dukkanin halin da ake ciki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta yi watsi da rahotannin da ke cewa an kai harin ƙunar baƙin wake a hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Laraba.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ya fitar.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi bayan jami'in hukumar EFCC ya salwantar da ransa

Ba a kai harin kunar bakin wake a hanyar Kaduna zuwa Abuja ba
Gwamnatin Kaduna ta musanta kai harin kunar bakin wake a hanyar Kaduna zuwa Abuja Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Jaridar Tribune ta ce Samuel Aruwan ya raba sanarwar ne ga manema labarai ranar Laraba a Kaduna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zancen harin bam a hanyar Abuja-Kaduna

Kwamishinan ya bayyana cewa ko kaɗan babu ƙamshin gaskiya a rahotannin da aka yaɗa kan harin ƙunar baƙin waken, rahoton Sahara Reporters ya tabbatar.

"Hankalin ma'aikatarmu ya kai kan rahotannin da ake ta yaɗawa, dangane da faruwar harin ƙunar baƙin wake ko makamancin haka a hanyar Kaduna zuwa Abuja."
"Ma'aikatar tana son ta fayyace cewa ya zuwa lokacin wannan sanarwar (ƙarfe 5:00 na yamma, Laraba 3 ga watan Yuli, 2024), babu wani abu makamancin harin ƙunar baƙin wake ko akasin haka da ya auku a hanyar Kaduna zuwa Abuja."
"Jami’an tsaro da majiyoyin leƙen asiri da ke kan hanyar suna gayawa gwamnati dukkanin halin da ake ciki.
"Rahotannin kai harin ba komai ba ne face zallar kuskure."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Sokoto ta fadi dalilin yin doka domin rage ikon Sarkin Musulmi

"Jami’an tsaron da aka girke a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja da ma yankin gaba ɗaya za su ci gaba da sanya ido domin tabbatar da tsaron ƴan ƙasa da matafiya."

- Samuel Aruwan

Ƴan bindiga sun hallaka ƴan gudun hijira

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu da ake zargin ƴan bindiga ne ɗauke da makamai sun kashe mutane uku a jihar Benue.

Mutanen dai waɗanda ke rayuwa a sansanin ƴan gudun hijira na Agagbe sun rasa rayukansu ne lokacin da suke dawowa daga gonakinsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel