Malamin Addini Ya Rasa Ransa Bayan Ɗansa Ya Sanadiyyar Ajalinsa Yana Bacci

Malamin Addini Ya Rasa Ransa Bayan Ɗansa Ya Sanadiyyar Ajalinsa Yana Bacci

  • Wani matashi ya hallaka mahaifinsa wanda babban Fasto ne mai suna Isaac Umurie yana tsaka da bacci a jihar Delta
  • Matashin mai suna Ufuoma Umurie yanzu haka yana hannun ƴan sanda wanda aka tabbatar yana fama da ciwon tabin hankali
  • Makwabtan Faston sun tabbatar da cewa wannan ba shi ne karon farko ba da ɗan ke farautar ran mahaifin nasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Delta - An shiga wani irin yanayi bayan ɗa ya kashe mahaifinsa yana tsaka da bacci.

Marigayin Isaac Umurie wanda babban Fasto ne ya rasa ransa bayan ɗansa ya yi ajalinsa yana bacci a jihar Delta.

Wani ya hallaka mahaifinsa wanda Fasto ne a Delta
Matashi ya yi ajalin mahaifinsa, Fasto Isaac Umurie a jihar Delta. Hoto: Legit.
Asali: Original

Delta: Matashi ya hallaka mahaifinsa

Kara karanta wannan

Kano: Ana fargabar mutane sun mutu yayin da gini ya rufta kansu ana ruwan sama

Lamarin ya faru ne da daren yau Laraba 3 ga watan Yulin 2024 a Okpare da ke karamar hukumar Ughelli ya Kudu, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wanda ake zargin mai suna Ufuoma Umurie ya kuma kai hari kan mahaifiyarsa da ta yi kokarin kare mijinta.

An ruwaito cewa da kyar mahaifiyarsa ta sha inda ta tsira da saran adda daga ɗan nata da tsakar dare.

Wasu majiyoyi sun tabbatar cewa wannan shi ne karo na biyu da ɗan ke farautar ran mahaifinsa a yankin.

Jama'a sun yi kokarin kawo dauki amma kafin zuwan su ma ɗan ya riga ya aikata laifin na kisan mahaifin nasa.

Martanin rundunar ƴan sanda a Delta

Kakakin rundunar ƴan sanda a jihar, Bright Edafe ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce Umurie yana hannunsu.

Edafe ya tabbatar da cewa ana zargin matashin yana fama da ciwon ƙwaƙwalwa inda aka fara bincike.

Kara karanta wannan

Yobe: Wata matar aure ta soka wa mijinta wuƙa har lahira, ta yi bayanin abin da ya faru

Ya tabbatar da cewa za a hukunta shi dai-dai da laifinsa da zaran an kammala bincike kan lamarin.

An kama masu garkuwa & matsafa a Delta

A wani labarin, kun ji cewa ƴan sanda a jihar Delta sun sanar da kama ƴan bindiga da ake zargin masu garkuwa ne da wasu matsafa dauke da gashin mutum.

Dan bindigar da aka fara kamawa mai suna Favour Eze, dan shekaru 24 ya fito ne daga ƙaramar hukumar Afikpo da ke jihar Ebonyi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin. \

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel