'Yan Sanda Sun Gurfana a Kotun Kano Saboda Zargin Satar N322m a Fashi da Makami

'Yan Sanda Sun Gurfana a Kotun Kano Saboda Zargin Satar N322m a Fashi da Makami

  • Wasu jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya sun gurfana gaban kotu a Kano saboda zargin fashi da makamin kudi masu tarin yawa
  • Ana zargin jami'an 'yan sanda uku: SP Yusuf Buba da Sufeto Rabiu Umar da kuma Sufeto Mukhtar Umar ’Yan Lilo da laifin fashi
  • Gwamnati na zarginsu da fashin N322m daga hannun wani bawan Allah mai suna Abdulrazak Sani, lamarin da suka ce ba haka ba ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano- Gwamnatin Kano ta maka wasu jami'an 'yan sanda guda uku a gaban kotu bisa zargin aikata fashi da makami a jihar.

Gwamnatin ta gurfanar da jami'an tsaron da wasu mutane uku da ake zargi da fashin makudan miliyoyi da ya kai N322m.

Kara karanta wannan

Tsaro: Sabon kwamishinan 'yan sandan Kano ya umarci sintirin jami'ai babu kakkautawa

Abba Kabir Yusuf
Gwamnatin Kano ta maka 'yan sanda kotu saboda zargin fashi da makami Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa ana zargin SP Yusuf Buba da Sufeto Rabiu Umar da kuma Sufeto Mukhtar Umar ’Yan Lilo da hada baki da wasu wajen aikata fashin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda 'yan sanda su ka buge da 'fashi'

Lauyar gwamnatin Kano, Barista Aishatu Salisu ta shaidawa kotu cewa ana zargin jami'an 'yan sandan guda uku da hada baki wajen kwatar N322m daga hannun Abdulrazak Sani.

Amma ta shaidawa kotun cewa jami'an sun mayar da wani kaso na kudin da ya kai N228m, amma har yanzu akwai sauran N97m.

Wadanda ake zargi sun musanta tuhumar fashi da makami da ake yi masu.

Wasu jami'an 'yan sanda sun ki halartar kotu

Lauyar gwamnati, Aishatu Salisu ta koka gaban kotu kan yadda rundunar yan sanda ta yi biris da bukatar kawo wasu daga jami'anta da ake zargi gaban kotu.

Kara karanta wannan

Kano: KEDCO ya yanke wutar lantarkin jami'ar Dangote saboda taurin bashi

Ta bayyana cewa duk da ta rubuta wasika ga rundunar domin tabbatar da jami'an yan sanda Rabiu Umar da Mukhtar Umar ’Yan Lilo sun gurfana gaban kotu, har yanzu ba su bayyana ba.

Amma lauyan wadanda ake kara, Barista A. U. Hajj, ya nemi kotu ta gudanar da shari'ar jami'in da ya hakarci kotun da wadanda ba su zo ba, kuma alkali ya amince da haka.

Yanzu haka an dage shari’ar zuwa ranar 19 ga watan Yuli, 2024.

Kano: Yan sanda sun kara yawan sintiri

A baya mun ruwaito cewa rundunar yan sandan Kano za ta kara tsaurara gudanar da sinitiri a jihar domin dakile ayyukan miyagu da damuna.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Salman Garba ne ya bayar da umarnin ganin yadda ake samun karuwar yawan ayyukan bata gari a wannan lokaci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel