Ana Tsakiyar Tsadar Fetur, NNPC Ya Ayyana Dokar Ta Ɓaci a Bangaren Haƙo Ɗanyen Mai

Ana Tsakiyar Tsadar Fetur, NNPC Ya Ayyana Dokar Ta Ɓaci a Bangaren Haƙo Ɗanyen Mai

  • A ranar Talata ne kamfanin man fetur na kasa (NNPC) ya kafa dokar ta baci kan danyen man da Najeriya ke hakowa
  • Shugaban kamfanin NNPC, Mele Kyari ne ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi a wani taro da ke gudana a Abuja
  • Mista Kyari ya ce an dauki matakin ne domin kara yawan danyen man da Najeriya ke hakowa da kuma bunkasa arzikinta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) ya bayyana cewa ya saka dokar ta baci dangane da hako danyen mai a kasar nan.

Kamfanin NNPC ya ayyana yaki da duk wasu abubuwan da ke kawo barazana ga hako danyen mai a Najeriya.

Kara karanta wannan

Jihohin Arewa 3 da aka samu sabani tsakanin sababbin gwamnoni da sarakunan gargajiya

NNPC ta yi magana kan harkar hako danyen mai a Najeriya
NNPC ya ayyana dokar ta baci kan hako mai a Najeriya. Hoto: @nnpclimited
Asali: Facebook

Mele Kyari, babban jami’in gudanarwa na kamfanin NNPC, ya bayyana hakan a ranar Talata a wajen bikin bude taron mai da iskar gas na Najeriya karo na 23 inji jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NNPC na iya hako ganguna miliyan 2

Mele Kyari ya ce kamfanin na da kayan aikin da zai yaki masu hana hako mai a Najeriya kuma za su hada kai da masu ruwa da tsaki wajen ganin an samu nasara a yakin.

Shugaban NNPC ya ce wani bincike da aka yi ya nuna cewa Najeriya na da karfin iya hako ganga miliyan biyu na danyen mai a kowace rana ba tare da tura sababbin na'urori ba.

Sai dai Mista Kyari ya ce gazawa wajen aiwatar da wasu tsare-tsare na daga cikin abin da ke kawo cikas ga cimma karfin hakar man.

Kara karanta wannan

Mutane 3 sun mutu, gidaje 50 sun lalace yayin da ruwan sama ya yi barna a jihar Arewa

Kamfanin NNPC ya ayyana dokar ta baci

Jaridar Premium Times ta ruwaito Mista Kyari ya ce ayyana dokar ta bacin zai taimaka wajen kara yawan danyen man da Najeriya ke hakowa da kuma bunkasa arzikinta.

“Mun yanke shawarar dakatar da tattaunawa a kan batun nan haka. A yanzu mun ayyana yaki a kan kalubalen da ke shafar hako danyen man da muke hakowa a kasar nan.
“Yaki na nufin yaki. Muna da kayan aikin da suka dace. Mun san abin da muka taka a karfin dukiya. Mun tuntubi abokan huldarmu, kuma za mu yi aiki tare domin samar da ci gaba."

NNPC ya fara hako mai a Akwa Ibom

A wani labarin, mun ruwaito cewa kamfanin NNPC tare da haɗakar kamfanin Olifield Services sun fara hako mai a sabuwar rijiya da ke jihar Akwa Ibom.

Takardar mai dauke da sa hannun jami'in yada labaran kamfanin Olufemi Soneye ta nuna cewa an fara hako man ne tun ranar 6 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

An shawarci gwamnati ta bude iyakokin shigo da abinci domin magance yunwa a Najeriya

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.