Majalisa Za Ta Binciki Tashin Bam a Borno, Ta Dora Laifin Kan Jama'ar Yankin
- Bayan harin kunar bakin wake da aka kai, majalisar wakilan Najeriya za ta binciki musabbabin tashin bama-bamai a Borno
- Hon. Ahmad Jaha, dan majalisa mai wakiltar mazaɓar Damboa/Gwoza/Chibok ya ɗora laifin harin kan jama'a da jami'an tsaro
- Ɗan majalisar ya ce sakaci ne ya sa lamarin ya faru domin kaya iri ɗaya 'yan kunar baƙin waken suka saka a lokacin kai farmakin
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Wani dan majalisar wakilai, Hon. Ahmad Jaha, ya ce tayar da bam da aka yi baya-bayan nan a jihar Borno ya faru ne sakamakon sakacin jami'an tsaro da mutanen yankunan.
Hon. Jaha, wanda ke wakiltar mazaɓar Damboa/Gwoza/Chibok a jihar Borno, ya sanar da hakan a zaman majalisar wakilan na ranar Talata.
Majalisa ta zauna a kan hare-haren bam
Premium Times ta rahoto cewa, dan majalisar ya jagoranci mahawara kan buƙatar binciken tagwayen bama-bamai da suka tashi a jihar Borno.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce wasu mata 'yan ƙunar bakin wake daga Boko Haram ne suka tayar da bama-baman.
"Akwai sakacin jami'an tsaro, jama'a" - 'Dan majalisa
Yayin jawabi kan hare-haren baya-bayan nan, Hon. Jaha yace daga jama'a har hukumomin tsaro sun saki jiki kan matsalar tsaro saboda suna ji kamar tsaron ya tabbata.
"Ba za mu ci gaba da yin sake ba. Sake ne ɗaya daga cikin dalilan da suka sa wannan abun ya faru a mazaɓata."
- Hon. Ahmad Jaha.
"Kaya iri ɗaya suka saka" - Jaha
Kamar yadda jaridar The Punch ta bayyana, Hon. Jaha ya ce ya kamata a ce an gane 'yan ƙunar baƙin wake ne saboda kaya iri ɗaya suka saka a ranar.
Hon. Jaha ya kara da cewa:
"Ina son mu sani cewa, bayan an gane fuksar masu ƙunar baƙin waken, an gano cewa daukar nauyinsu aka yi, aka zuga su kuma aka shigar da su Gwoza daga wani wurin.
“Sun zo cikin shigar kaya iri ɗaya. Kaya kala ɗaya suka saka. Wannan kira ne da zai zaburar da kowa a ƙasar nan. Idan ka ga irin wannan abu, to barazanar tsaro ce.
“Akwai tsananin buƙatar hukumomin tsaro su inganta bincikensu na sirri tare da haɗa guiwa da mazauna yankuna domin gujewa sake faruwar irin wannan lamarin a gaba."
Ƙarin mutum 2 sun mutu a harin Borno
A wani labari na daban, wasu ƙarin mutum biyu sun riga mu gidan gaskiya, daga cikin mutane 42 da ke asibiti sakamakon harin bam a Borno.
Hakan ya kai adadin waɗanda suka rasa rayukansu zuwa 20 a harin ƙunar bakin waken da ya faru wanda ake zargin aikin 'yan Boko Haram ne.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng