"Dalibai 300,000 Ake Sa Ran Za Su Nemi Lamunin Karatu" Inji NELFund
- Hukumar kula da asusun ba daliban kasar nan lamunin karatu ta bayyana cewa akalla daliban kasar nan 300, 000 ne za su nemi lamuni
- Manajan daraktan hukumar, Akintunde Sawyerr ne ya bayyana haka, inda ya ce akwai shirin ba dalibai akalla miliyan biyu dama
- Sawyerr ya kara da cewa daliban za su biya kudin idan sun kammala karatyu kuma sun kama aiki, inda za a rika tsakura daga abashinsu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja- Hukumar kula da asusun ba dalibai rancen kudin karatu NELFund ta ce ana sa ran daliban kasar nan akalla 250,000 zuwa 300,000 ne za su nemi lamunin karatu.
Manajan daraktan hukumar, Akintunde Sawyerr ne ya bayyana haka, inda ya ce sun kammala shirin ba su damar karbar lamunin.
Jaridar Leadership ta wallafa cewa ana sa ran daliban da ke karatu ne za su fi neman lamunin idan aka kwatanta da matasam Najeriya wasu bangarorin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Mun shirya ba dalibai lamuni" - NELFund
Shugaban hukumar, Akintunde Sawyerr ya bayyana cewa akwai isassun kudin da za a ba daliban kasar lamunin karatu.
Mista Sawyerr ya ce akwai kyakkyawan shirin ba daliban manyan makarantun Najeriya akalla miliyan biyu tallafin domin su gudanar da karatunsu.
Daliban jami'a za su samu damar karatu
Daliban sun fito daga makarantu masu zaman kansu da na gwamnati, kuma gwamnati ta samar da lamunin ne domin saukaka masu samun ilimi.
Ya kara da cewa daliban za su biya bashin karatun ne idan sun fara aiki, kuma za a fara yankar kudin kai tsaye daga albashinsu.
"Dalibai za su samu lamunin karatu," NelFund
A wani labarin kun ji cewa gwamnatin tarayya ta bayyana cewa duk daliban da su ka cancanci samun lamunin karatu za su samu.
Babban daraktan hukumar a bangaren kudi da gudanarwa, Dr. Fred Akinfala ne ya bayyana haka, inda ya ce ba sai da uban gida ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng