Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Bindiga a Jihohi, Sun Kama Manyan 'Yan Ta’adda
- Rundunar sojin Najeriya ta kai farmaki kan taron manyan yan ta'adda a jihohin Imo da Kwara domin dakile ayyukan barna
- Farmakin ya ba sojojin Najeriya nasarar cafke wasu manyan yan ta'addan da suka fitini al'umma da ayyukan ta'addanci
- Har ila yau, rundunar sojin ta bayyana irin makaman da ta kwace wajen yan ta'addar a yayin farmakin da ta kai a kansu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Imo, Kwara - Rundunar sojin Najeriya ta kai farmaki kan yan ta'adda a jihohin Imo da Kwara.
Farmakin na cikin kokarin da sojojin Najeriya ke yi domin yaki da ta'addanci da tayar da kayar baya.
Legit gano haka ne a cikin wani sako da rundunar sojin Najeriya ta wallafa a shafinta na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun kama yan ta'adda a Imo
Sojin Najeriya sun kai farmaki kan ƴan ta'addar IPOB a karamar hukumar Orlu a jihar Imo inda suka kama wasu daga cikin manyan yan kungiyar.
Daga cikin wadanda aka kama akwai Izuchukwu Emejuru, Chibozor Chikwe tare da kwato bindigogin zamani da na gargajiya a tattare da su.
Sojoji sun kama yan ta'adda a Onuimo
Haka zalika, rundunar sojin ta kai samame a karamar hukumar Onuimo a jihar ta Imo inda ta kama wani dan kungiyar IPOB da ake kira da Bam Bam.
Rundunar ta kuma kai wani farmaki kan yan ta'addar IPOB a karamar hukumar Okigwe a jihar Imo inda ta fatattakesu tare da kwato makamai.
'Dan ta'adda ya fada hannun sojoji a Kwara
A wani farmaki da rundunar sojin Najeriya ta kai ƙaramar hukumar Edu a Kwara, ta kama wani dan bindiga mai suna Ibrahim Abdullahi.
Ana zargin Ibrahim Abdullahi da ayyukan ta'addanci a jihar kuma an kwato bindigogi da sauran makamai a hannunsa.
Sojoji sun kama masu leken asiri
A wani rahoton, kun ji cewa sojoji sun kama wasu mata uku masu tallar zuma a bakin titin bisa zargin yiwa ƴan bindiga leƙen asiri a jihar Kaduna.
Rahotanni sun nuna cewa an kama waɗanda ake zargin ne a kusa da kauyen Dogon Daji da ke ƙaramar hukumar Kagarko.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng