Bayan Tashin Bama Bamai a Borno, Sojoji sun Kashe 'Yan Ta'adda Har Maboyarsu

Bayan Tashin Bama Bamai a Borno, Sojoji sun Kashe 'Yan Ta'adda Har Maboyarsu

  • Dakarun hadin gwiwa na kasashe masu yaki da Boko Haram (MNJTF) sun kai mummunan hari kan maboyar 'yan ta'adda a iyakokin Kamaru da tafkin Chadi
  • Rundunar ta kashe yan ta'adda kimanin 70 awanni bayan wani harin bakin wake da ake zargin 'yan Boko haram sun kai Gwoza tare da kashe mutane da yawa
  • Rundunar sojojin ta bayyana samun nasara, tare da lalata makaman yan ta'addan, yayin da wasu da yawa su ka tsere neman mafaka a sassa daban-daban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Borno- Kwana guda bayan kai harin kunar bakin wake kan masu murnar daurin aure a Gwoza da ke jihar Borno, dakarun hadin gwiwa na kasashe masu yaki da Boko Haram (MNJTF) ta fatattaki 'yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Sojoji sun ragargaji yan bindiga a jihohi, sun kama manyan 'yan ta'adda

A harin da rundunar ta kai maboyar yan ta'addan da ke yankin tafkin Chadi, an kashe miyagu kimanin 70.

Sojoji
Sojojin hadin gwiwa sun kashe 'yan ta'adda 70 Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta wallafa cewa ruwan alburusai ta sama da kasa da sojojin su ka yi amfani da su ya ba su nasarar lalata abubuwan fashewa guda takwas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun tarwatsa maboyar 'yan ta'adda

A sanarwar da jami'in hulda da jama'a na rundunar MNTJF, Laftanal Kanal Abdullahi Abubakar ya fitar, ya ce harin hadin gwiwar wani bangare ne na aikin kakkabe miyagu.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa rundunar ta yi fata-fata da maboyar 'yan ta'addan a iyakokin Kamaru da tafkin Chadi da ke makwabtaka da kasar nan, tare da lalata makamai da dama.

Dakarun hadin gwiwar da sun hada da sojojin Najeriya, Nijar da Kamaru ne su ka kai hare-haren da ya sanya wasu 'yan ta'adda tserewa.

Kara karanta wannan

Harin bam: Rundunar sojojin Najeriya ta fadi yadda za ta yi da 'yan ta'adda

Harin Gwoza: Wasu sun kara rasuwa

A baya mun kawo labarin cewa an samu karuwar wadanda su ka rasu a harin kunar bakin waken da miyagu su ka kai Gwoza da ke Borno.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta bayyana cewa mutanen da su ka rasu yanzu sun kai 18, yayin da wadanda su ka ji rauni ke jinya a asibiti.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.