Lokaci Ya Yi: Wata Hajiya Daga Jihar Neja Ta Rasu a Saudiyya
- Allah ya yiwa wata Hajiya da ta fito daga jihar Neja da ke yankin Arewa ta Tsakiya na Najeriya rasuwa yayin gudanar da aikin Hajjin bana na shekarar 2024
- Marigayiyar mai suna Hajiya Adeshatu Abubakar ta rasu ne a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya bayan ta dawo daga masallacin Harami a daren ranar Asabar, 29 ga watan Yunin 2024
- Sakataren hukumar jin daɗin Alhazan jihar wanda ya tabbatar da rasuwar marigayiyar a cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce ta rasu ne sakamakon tsananin zafi bayan ta riƙa fitar da jini ta hanci da baki
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Neja - Hukumar jin daɗin Alhazai ta jihar Neja ta sanar da rasuwar wata Hajiya daga cikin Alhazan jihar a ƙasar Saudiyya.
Marigayiyar mai suna Hajiya Adeshatu Abubakar ta rasu ne a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya.
Wata sanarwa da sakataren hukumar, Mohammad Aliyu, ya fitar a ranar Lahadi ta tabbatar da rasuwar marigayiyar, cewar rahoton jaridar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hajiya daga Neja ta rasu a Saudiyya
Mohammad Aliyu ya bayyana cewa Hajiya Adeshetu Abubakar, ta rasu ne da misalin karfe 11:00 na daren ranar Asabar, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar.
"Hajiya Adeshetu Abubakar, mai shekara 65 a duniya, ta fito daga ƙaramar hukumar Bida. Ta rasu ne ƴan sa'o'i kaɗan bayan ta dawo daga masallacin Harami."
"Ta sauko daga daƙinta zuwa gaban hotel ɗin da take zaune, sai ta faɗi sannan ta fara fitar da jini ta hanci da baki da sauransu. Ta rasu nan take domin ƙoƙarin ceto ranta da aka yi bai yi nasara ba."
"Ba a santa da ciwon hawan jini ko siga ba. An tabbatar da rasuwarta da misalin ƙarfe 11:40 na daren ranar Asabar. Ta rasu ne sakamakon tsananin zafi."
"Allah ya yafe mata kura-kuranta ya kuma sanya ta a Aljannah Firdaus."
- Mohammad Aliyu
A yayin aikin Hajjin bana na shekarar 2024, akwai Alhazan Najeriya da suka riga mu gidan gaskiya.
Alhazan jihar Kebbi sun rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu Alhazai biyu daga jihar Kebbi, Hajiya Maryamu Mayalo da Alhaji Malami Besse na Koko Besse sun riga mu gidan gaskiya.
Yayin da Hajiya Maryamu ta ƙaramar hukumar Maiyama ta rasu bayan doguwar jinya a Makka, Alhaji Malami ya rasu a Kebbi a ranar Lahadi jim kaɗan bayan dawowarsa daga Saudiyya.
Asali: Legit.ng