Rundunar Sojojin Saman Najeriya Ta Musanta Hatsarin Jirginta, Ta Fadi Abin da Ya Faru

Rundunar Sojojin Saman Najeriya Ta Musanta Hatsarin Jirginta, Ta Fadi Abin da Ya Faru

  • Rundunar sojin saman Najeriya tace babu jirginta mai saukar ungulu da ya yi haɗari a safiyar Litinin
  • Kakakin rundunar ya tabbatar da cewa jirgi mara matuƙi ne yayi hadari a kauyen Rumji, inda babu nisa da sansaninta
  • Edward Gabkwet ya ce wannan ƙaramin koma-bayan ba zai tsayar da ayyukan da rundunar ke yi ba na tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Rundunar sojin saman Najeriya ta ce wani daga cikin jiragenta na sama mara matuƙi ne ya yi haɗari a Kaduna, ba jirgin samanta mai saukar ungulu ba.

Ta kuma ƙara da cewa, ta fara bincike don tabbatar da abinda ka iya kawo haɗarin, inda ta ƙara da cewa babu ko mutum ɗaya da ya samu rauni tun bayan rikitowar jirgin.

Kara karanta wannan

Jirgin sojojin saman Najeriya ya yi hatsari, dakaru sun hallara a kauyen Kaduna

Rundunar sojin sama ta musanta yin hadarin jirginta mai saukar ungulu a Kaduna.
Rundunar sojin saman Najeriya ta musanta rahoton faɗuwar jirginta. Hoto: Nigeria Air Force
Asali: Facebook

Kakakin rundunar, Air Vice Marshal Edward Gabkwet, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin kuma aka wallafa a shafin rundunar na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jirgin rundunar sojin sama ya yi hatsari?

Wani sashe na sanarwar ya ce:

"Rahotannin da ke yawo a shafukan sada zumunta cewa jirgin rundunar sojin sama mai saukar ungulu yayi haɗari a Kaduna a safiyar yau, 1 ga Yulin 2024 ba gaskiya bane.
"Wani jirgin rundunar ne mara matuƙi ya fuskanci matsala bayan ya tashi domin fara aiki a kusa da ƙauyen Rumji mai nisan kilomita 15 daga sansaninmu."

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

"Tun da jirgi ne mara matuƙi, babu wanda ya samu rauni a sama ko a ƙasa. An fara bincike kan lamarin domin gano abin da ya jawo haɗarin."

Rahoton farko na hatsarin jirgin sojoji

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka sace basarake da wasu bayin Allah a Arewa

A safiyar Litinin din nan ne rahotanni suka karade cewa jirgin saman rundunar sojin mai saukar ungulu ya samu matsala a sama kuma ya fadi a yankin Igabi ta jihar Kaduna.

Wani ganau ba jiyau ba wanda ya buƙaci a boye sunansa ya bayyana cewa lamarin ya faru wurin ƙarfe 5 na subahi, lamarin da ya tashi hankalin mazauna yankin.

Artabun jami'an tsaro da 'yan bindiga

A wani rahoto na daban, mun ruwaito cewa an yi ruwan alburusai tsakanin jami'an tsaro da miyagun 'yan bindiga a babban birnin tarayyar Najeriya ta Abuja.

Lamarin mara daɗi ya faru ne a yankin Bwari da ke babban birnin tarayyar inda 'yan bindigan suka yi yunƙurin garkuwa da wasu kananan yara mata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel