Mahaifiyar Tsohon Gwamnan Borno Ta Rigamu Gidan Gaskiya, Shehu Sani Ya Yi Ta’aziyya
- Rahotanni sun bayyana cewa mahaifiyar tsohon gwamnan jihar Borno kuma jigo a jam'iyyar APC, Ali Modu Sheriff ta kwanta dama
- An ce marigayiya Hajiya Aisa ta rasu ne a ranar Lahadi bayan doguwar jinya a wani asibitin Abuja, kuma ta rasu tana da shekaru 93
- Tsohon sanatan Kaduna, Shehu Sani ya aika sakon ta'aziyya ga Sanata Ali Sheriff kan wannan babban rashi da ya yi na mahaifiyarsa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Borno - Mun samu labarin rasuwar Hajiya Aisha, mahaifiyar tsohon gwamnan jihar Borno kuma jigo a jam'iyyar APC, Ali Modu Sheriff.
An ruwaito cewa Hajiya Aisa ta kwanta dama ne a ranar Lahadi bayan doguwar jinya a wani asibitin Abuja, kuma ta rasu tana da shekaru 93 a duniya.
Mahaifiyar Ali Modu Sheriff ta rasu
Zagazola Makama ne ya sanar da mutuwar mahaifiyar tsohon gwamnan a shafinsa na X, inda ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Mahaifiyar Sanata Ali Modu Sheriff, tsohon gwamnan jihar Borno, ta rasu.
Ya Hajja ta rasu a yau (Lahadi) tana da shekaru 93 a duniya."
Jana'izar mahaifiyar Ali Modu Sheriff
Wani ma'abocin shafin X, @BMB1_Official ya sanar da cewa an shirya gudanar da jana'izar marigayiyar a ranar Litinin, 1 ga Yuli a bayan sallar Azuhur.
Za a gudanar da jana'izar mahaifiyar ne a gidan marigayi Galadima Modu Sheriff da ke titin Damboa, garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Shehu Sani ya yiwa Ali Sheriff ta'aziyya
A safiyar yau Litinin, tsohon sanatan Kaduna, Shehu Sani ya aika da sakon ta'aziyya ga Sanata Ali Modu Sheriff kan wannan babban rashi da ya yi.
Ina mika sakon ta'aziyyata ga Sanata Ali Modu Sheriff bisa rasuwar mahaifiyarsa, muna rokon Allah ya sanyata a gidan Aljannar Firdausi, amin."
- Inji Sanata Shehu Sani.
Ali Sheriff ya hakura da shugabancin APC
A wani labarin a baya, mun ruwaito cewa Sanata Ali Modu Sheriff ya janye daga takarar kujerar shugabancin jam'iyyar APC na kasa gabanin babban taronta da ta gudanar.
Tsohon gwamnan na jihar Borno ya ce ya janye ne saboda tsarin yanki na jam'iyyar wacce ta mika kujerar ga arewa ta tsakiya kuma zai yi biyayya ga wanda aka zaba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng