An Samu Karin Mutanen da Suka Mutu a Harin Bam da Aka Kai Jihar Borno

An Samu Karin Mutanen da Suka Mutu a Harin Bam da Aka Kai Jihar Borno

  • Rahotanni sun bayyana cewa mutum biyu daga cikin 42 da aka kwantar a asibiti sakamakon harin bam a Gwoza sun mutu
  • Da mutuwar mutane biyun, ana fargabar mutum 20 ne suka mutu a wannan mummunan harin kunar bakin wajen a jihar Borno
  • Mukaddashin gwamnan jihar, Alhaji Umar Kadafur ya jaddada cewa wannan harin ba zai kawo nakasu a yaki da ta'addanci ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Maiduguri, Borno - An samu rahoton cewa wasu mutane 2 da harin bam na Gwoza ya rutsa da su sun rasa rayukansu a lokacin da ake jinyarsu a asibitin kwararru na Maiduguri.

An tattaro cewa daga cikin mutane 42 da suka jikkata da aka kwantar a asibiti, an sallami 16 daga cikinsu yayin da 24 ke jinya a asibitin har yanzu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun buɗe wa matafiya wuta, sun yi awon gaba da mutane 20 a kan titi

Gwamnati ta yi magana kan harin bam a jihar Borno
Adadin mutanen da suka mutu a harim bam na Borno ya kai 20. Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

Adadin mutanen da suka mutu ya kai 20

An bayyana hakan ne a wata ziyara da mukaddashin gwamnan Borno, Alhaji Umar Kadafur ya kai asibitin ranar Lahadi, kamar yadda Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kadafur ya ce duk da wannan mummunan harin, dole ne a ci gaba da yaki da ta'addanci da 'yan ta'adda a jihar ba tare da gajiyawa ba.

A yayin da ake fargabarar adadin wadanda suka mutu a harin ya kai 20 zuwa yanzu, mataimakin gwamnan yayi Allah wadai da hare-haren da ake kaiwa jama'a.

Ya ce wadanda suka aikata wannan aika-aikan sun yi amfani da sakin jikin da jama'ar yankin suka yi kan matsalar tsaro, sakamakon zaman lafiya da aka samu a jihar.

Gwamnati ta yi kira ga mutanen Borno

Mukaddashin gwamnan ya yi kira ga jama’a da su kara taka tsan-tsan tare da kai rahoton duk wanda basu yarda da shi ba ga jami’an tsaro domin gudun faruwar irin hakan a gaba.

Kara karanta wannan

Borno: Mutane sun mutu bayan wata ta kai harin bam kan masu zaman makoki

An ce Kadafur ya samu rakiyar Sanata Ali Ndume, Ahmadu Jaha mai wakiltar mazabar Damboa, Gwoza da Chibok, da sauran jami'an gwamnati.

Ya sanar da cewa gwamnatin jihar ta biya kudaden jinyar wadanda abin ya shafa yayin da ya ba da tabbacin zasu samu isasshen kulawar lafiya.

An kai harin bam kauyen Borno

Tun da fari, mun ruwaito cewa wata 'yar kunar bakin wake ta tayar da bam a garin Gwoza yayin da wasu jama'a suke zaman makoki a ranar Asabar, 29 ga Yuni.

Kwamishinan 'yan sanda a jihar, Yusuf Lawal ya tabbtar da faruwar lamarin inda ya ce mace ce ta tayar da bam din, kuma mutane da dama sun mutu yayin da wasu suka jikkata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.