'Yan Bindiga Sun Buɗe wa Matafiya Wuta, Sun Yi Awon Gaba da Mutane 20 a Kan Titi
- Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga sun tare wata motar fasinjoji a titin Sagamu-Ijebu-Ode inda suka yi awon gaba da mutane
- Wani mazaunin yankin Ilishan ya shaidawa manema labarai cewa 'yan bindigar sun harbi wani a guiwarsa, yanzu yana asibiti
- An yi kira ga jama'a musamman wadanda suka san 'yan uwansu sun fi ta hanyar Sagamu da su tuntube su domin jin ko suna lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Ogun - Kimanin matafiya 20 ne rahotanni suka ce wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da su a hanyar Sagamu-Ijebu-Ode.
An ce 'yan bindigan sun yiwa matafiya kwanton bauna ne a ranar Lahadi a kusa da yankin ofishin 'yan sandan Sagamu da Ilishan.
'Yan bindiga sun farmaki matafiya
Wani mazaunin yankin kuma shugaban kungiyar ci gaban Ilishan, Wemmy Osude, ya ce an harbi wani matafiyi a gwiwa a lokacin da lamarin ya faru, in ji rahoton Channels.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai kuma an ce jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a jihar, Omolola Odutola ya ce rahoton ba gaskiya ba ne.
Amma Mista Wemmy Osude ya tabbatar da cewa daya daga cikin wadanda harin ya rutsa da su, mazaunin Ilisan Remo, yana kwance a asibitin koyarwa na jami’ar Babcock yanzu haka.
A cewar Osude:
“An harbi wani mazaunin Ilisan a gwiwarsa kuma yana samun kulawa a asibitin koyarwa na Babcock."
An yi garkuwa da matafiya a Ogun
Jaridar Vanguard ta ruwaito Osude wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya kuma bayyana cewa ya yi magana da kwamandan ‘yan sanda na yankin Sagamu kan lamarin.
"Yan bindigan sun tafi da mutane da dama zuwa cikin daji. Idan kuna da 'yan uwa da suka taso kuma ta hanyar nan za su bi ku tuntube su ku ji ko suna lafiya.
"Na yi magana da kwamandan yankin Sagamu game da wannan lamarin, kuma mu na da yakinin cewa jami'an tsaro za su bi wadannan miyagu tare da kubutar da wadannan mutane."
An sace matafiya a hanyar Abuja
A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu gungun 'yan bindiga sun tare motocin matafiya daga Enugu zuwa babban birnin tarayya Abuja, inda suka tafka barna.
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Nasarawa, DSP Ramhan Nansel ya ce lamarin ya faru ne a kan titin Nasarawa-Keffi, kuma an sace mutane da dama.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng