"Kar a Bari Rashin Tsaro ya Kara Kamari a Arewa," Atiku Abubakar

"Kar a Bari Rashin Tsaro ya Kara Kamari a Arewa," Atiku Abubakar

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi tir da harin kunar bakin wake da ya kashe mutane da dama a Gwoza yayin bikin aure
  • Wata mace dauke da goyo a bayanta ce ta tayar da bam ɗin a harin kunar bakin waken da ya kashe akalla mutane 18, yayin da wasu suka ji raunuka
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar na ganin gazawar gwamnatin Tinubu wajen magance matsalar tsaro duk da nasarar da aka samu a baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Borno- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana alhini kan harin kunar bakin wake da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 18.

Kara karanta wannan

Borno: Mutane sun mutu bayan wata ta kai harin bam kan masu zaman makoki

Wata mace dauke da goyo ce ta tayar da bam ɗin a wajen bikin aure a Gwoza da ke jihar Borno, lamarin da ya jawo hankali duniya saboda muninsa.

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar ya bayyana takaici kan harin bam a Borno Hoto: Atiku Abubakar/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Atiku Abubakar, a sakon da ya wallafa a shafinsa ya Facebook ya bayyana alhininsa kan mummunan lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Rashin tsaro na kokarin dawowa" - Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa ya ce abin takaici ne matuka yadda rashin tsaro ke dawo wa Arewa maso gabashin kasar nan, kamar yadda Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa.

Atiku Abubakar ya ce harin ya kara nunawa karara cewa gwamnatin Tinubu ta gaza, inda ya ce bai kamata a ce an yi asarar nasarar da aka samu a baya kan tsaro ba.

Tsohon mataimakin shugaban ya zaburar da gwamnatin tarayya ta dauki matakan da su ka dace domin magance rashin tsaro da ke kara ruruwa a Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Ruwa ya cinye wasu dalibai a hanyarsu ta dawo wa daga jarrabawa a Kaduna

Ya kuma mika ta'azziyyarsa ga iyalan wadanda iftila'in ya rutsa da addu'ar Allah ya gafartawa wadanda su ka rasu.

Wasu sun kara mutuwa a harin Borno

A wani labarin, kun ji cewa an samu karuwar wadanda suka rasa rayukansu a harin kunar bakin wake a Gwoza, jihar Borno.

Adadin waɗanda suka rasu a yanzu sun kai 18 a harin bakin wajen da ake zargin kungiyar 'yan ta'addan boko haram sun kai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.