Dakarun Sojojin Sama Sun Yi Ruwan Wuta Kan 'Yan Ta'adda da Barayin Man Fetur
- Dakarun rundunar sojojin saman Najeriya sun samu nasara kan ɓarayin man fetur da ƴan ta'adda a wasu hare-hare da suka kai
- Sojojin saman sun lalata haramtattun wuraren tatar mai da ɓarayin suke amfani da su a jihar Rivers da ke yankin Neja Delta
- Hakazalika sojojin sun yi ruwan wuta kan ƴan ta'adda a jihar Neja inda suka hallaka da dama daga cikinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Hare-haren da dakarun rundunar sojojin sama suka kai sun lalata haramtattun wuraren tatar mai a jihar Rivers.
Haren-haren saman sun kuma hallaka ƴan ta'adda masu yawa da ke kan babura a jihar Neja.
Daraktan hulɗa da jama'a da yaɗa labarai na rundunar, AVM Edward Gabkwet shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, cewar rahoton jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojojin sama sun tarwatsa ɓarayin mai
Edward Gabkwet ya bayyana cewa ɓarayin man fetur ɗin na ci gaba da kawo sababbin dabaru na aikata ɓarnar da suke yi a yankin Neja Delta.
Ya nuna cewa hakan ya sanya rundunar da sauran hukumomin tsaro suka ƙara zage damtse tare da yin amfani da kayan aiki na zamani domin samun damar gano ayyukan ɓata garin.
Ya bayyana cewa dakarun sojojin na Operation Delta Safe sun lalata haramtattun wuraren tatar mai guda uku a Wilcourt, wani gari da ke bakin ruwa a yankin Neja Delta.
Sojoji sun hallaka ƴan ta'adda
Edward Gabkwet ya kuma bayyana cewa an samu nasarar hallaka ƴan ta'adda da ke ɓoye a Dandunu bayan sun saci dabbobi a ƙauyukan da ke yankin Kuchi-Kapana a ƙaramar hukumar Munya ta jihar Neja.
Ya bayyana cewa bayan samun bayanai sirri kan ayyukan ƴan ta'addan, an tura jirage domin duba yankin, inda suka hango ƴan ta'addan a kan babura tara suna tafiya da dabbobin.
"Jiragen sun yi luguden wuta kan ƴan ta'addan da ke tafiya a kan baburan, inda da yawa daga cikinsu suka rasa rayukansu."
- Edward Gabkwet
Sojojin sama sun hallaka ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojin saman Najeriya ta ce dakarun Operation Hadarin Daji sun kai samame ta sama kan wasu manyan ƴan bindiga biyu a jihohin Katsina da Zamfara.
Sojojin saman sun kai samamen ne kan sansanin ƙasurgumin ɗan bindiga, Maudi Maudi a Kudancin ƙauyen Tsaskiya, ƙaramar hukumar Safana a Katsina.
Asali: Legit.ng