Tsohon Jigon APC Ya Wanke Tinubu Kan Halin da Arewa Ke Ciki, Ya Fadi Mai Laifi
- Salihu Mohammed Lukman ya yi magana kan halin da yankin Arewacin Najeriya ya samu kansa a ciki a wannan lokacin
- Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, ya ce ko kaɗan Shugaba Bola Tinubu ba shi da laifi kan halin da yankin yake ciki
- Ya nuna cewa yankin Arewa ya ɓarar da damarsa a lokacin mulkin Muhammadu Buhari wanda ya kasa farfaɗo da yankin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Salihu Mohammad Lukman ya wanke shugaban ƙasa Bola Tinubu daga zargi kan rashin ci gaba da ƙalubale iri-iri da ke fuskantar yankin Arewacin ƙasar nan.
Salihu Lukman ya ce yankin ya rasa damarsa a shekara takwas na mulkin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya kasa farfaɗo da yankin a lokacin mulkinsa.
Lukman ya wanke Tinubu daga zargi
Tsohon ɗan jam'iyyar ta APC ya wanke Tinubu a wata wasiƙa da ya rubuta wa shugabannin siyasar Arewacin Najeriya kuma ya rabawa manema labarai a Abuja ranar Lahadi, 30 ga watan Yuni, cewar rahoton jaridar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Salihu Lukman ya koka kan yadda rayuwa ta koma a Arewacin Najeriya a halin yanzu, rahoton jaridar The Guardian ya tabbatar.
"Idan mutum yana son ganin haƙiƙanin ma'anar rayuwar kaɗaici, talauci, mara kyau, kawai ya duba yadda rayuwa take a Arewacin Najeriya."
"Masarautunmu masu daraja da ƙima an rage darajarsu. Da yawa daga cikin malaman addininmu sun saki hanyar Allah."
"Masana'antu ƴan kaɗan ne kawai akwai a yankin. Sannan saboda rashin tsaro, ayyukan noma wanda shi ne jigon tattalin arziƙin yankin ya zama koma baya."
"Abin takaici, ga mu yanzu a mulkin Tinubu wanda ya samu mafiya yawan ƙuri'u daga yankin waɗanda suka sanya ya lashe zaɓe amma kawai ya nuna yana son cin gajiyar rashin haɗin kan da ke tsakanin shugabannin yankin."
"Tabbas ba laifinsa ba ne, sannan idan bai nuna ya damu da magance ƙalubalen da yankin ke fuskanta ba, ka da wanda, musamman shugabannin siyasar Arewa, ya yi ƙorafi."
- Salihu Lukman
Salihu Lukman ya yi murabus daga APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar APC na ƙasa a yankin Arewa maso Yamma, Salihu Lukman ya yi murabus daga jam'iyyar.
Salihu Lukman ya zargi jamiyyar da rashin iya shugabanci da kuma munanan tsare-tsare wanda ya jefa ƙasar nan a cikin halin ƙunci.
Asali: Legit.ng