Za a Dauke Wutar Lantarki Na Watanni 2 a Wasu Jihohi 2, BEDC Ya Yi Karin Bayaniv
- Hukumar rarraba wutar lantarkin Najeriya ya sanar da shirin gudanar da muhimmin aikin gyara kan layin wutar Akure Osogbo
- A cewar sanarwar da kamfanin BEDC ya fitar, gyaran zai jawo daukewar wutar lantarki a jihohin Ondo da Ekiti na watanni biyu
- Sanarwar ta kara da cewa za a rika dauke wutar na awanni tara kullum a jihohin da abin ya shafa daga 1 ga Yuli zuwa 31 ga Agusta
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Masu amfani da wutar lantarki a jihohin Ondo da Ekiti za su kasance cikin rashin wutar lantarki na tsawon watanni biyu.
Za su kasance cikin duhu ne sakamakon gyaran da hukumar kula da rarraba wuta (TCN) za ta yi a kan layin Osogbo/Akure – Ado – Ekiti mai karfin 132kV.
Watanni 2 na rashin wuta a jihohi 2
A cewar sanarwar da kamfanin rarraba wuta na BEDC ya wallafa a shafinsa na X, aikin gyaran zai fara aiki ne daga ranar 1 ga Yuli zuwa 31 ga Agusta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An cewar sanarwar:
“Muna sanar da ku cewa kamfanin rarraba wutar lantarkin Najeriya (TCN) zai gudanar da muhimmin aikin gyara ga layin sadarwa na Akure Osogbo mai karfin 132kV.
"Aikin da aka tsara ya haɗa da shigar da wayar OPGW a karkashin kasa. Wannan zai buƙaci katse wuta a kan hanyar sadarwar da abin ya shafa yayin gudanar da aikin."
Lokacin da za a dauke wutar lantarkin
Jihohin da abin ya shafa sun hada da Ondo da Ekiti tare da daukewar wutar lantarki ta awanni 9 na safiya daga karfe 8 na safiya zuwa karfe 5 na yamma a kullum.
Sanarwar BEDC ta bayyana cewa abokan huldar kamfanin a yankunan da abin ya shafa za su fuskanci katsewar wutar a lokacin da aka tsara.
"Muna matukar ba da hakuri kan rashin jin dadin da wannan matakin zai iya haifarwa kuma muna neman afuwa da fahimtar ku."
- Inji BEDC.
Duba sanarwar a nan kasa:
Gwamnati za ta janye tallafin lantarki
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta fara shirye-shiryen janye tallafin wutar lantarki kamar yadda ta janye tallafin man fetur a 2023.
Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa Najeriya ba za ta iya ci gaba da biyan tallafin wutar lantarki ba don haka akwai bukatar janye tallafin gaba daya.
Asali: Legit.ng