Rarara: Malamin Musulunci Ya Soki Masu Murna da Sace Dattijuwa, Ya Ba da Shawara

Rarara: Malamin Musulunci Ya Soki Masu Murna da Sace Dattijuwa, Ya Ba da Shawara

  • Yayin da wasu ke murnan sace mahaifiyar mawaki Rarara, malamin Musulunci ya caccake su inda ya ce haka ba Musulunci ba ne
  • Sheikh Ishaq Adam Ishaq ya bayyana takaici yadda wasu ke murnan sace dattijuwar inda ya ce babu wanda ya tsira daga haka
  • Ya shawarci al'ummar Musulmi da su yi addu'ar Allah ya kubutar da ita da sauran wadanda aka kama madadin murna game da haka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ishaq Adam Ishaq ya magantu kan sace mahaifiyar mawaki Rarara.

Shehin malamin ya soki wandanda suke murna da hakan inda ya ce ba koyarwar Musulunci ba ne.

Kara karanta wannan

"Munafurci ne": Jarumar fim ta caccaki Kiristoci kan murnan auren mawaki Davido

Malamin Musulunci ya magantu kan sace mahaifiyar mawaki Rarara
Malamin Musulunci ya ba masu murnan sace mahaifiyar mawaki Rarara shawara. Hoto: Sheikh Barr. Ishaq Adam Ishaq, Dauda Kahutu Rarara.
Asali: Facebook

Rarara: Malamin Musulunci ya ba Musulmi shawara

Sheikh Ishaq ya bayyana haka a cikin wani karatu da aka yada faifan bidiyon a shafin X a jiya Asabar 29 ga watan Yunin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Bari in baku misali, akwai wani mawaki da masu garkuwa suka shiga har garinsu suka sace mahaifiyarsa, babu musiba da tafi haka."
"A matsayinka na Musulmi abin da ya kamata ka yi shi ne addu'ar Allah ya kubutar da ita lafiya saboda kai ma iyayenka ba su tsira ba."
"Amma naga wasu maza da mata murna suke yi, wasu su ce Allah yasa a kashe ta a mata kaza da kaza, wannan fa tsohuwa ce mai shekaru 70."
"Kuma hakan ba zai wuce dayan biyu ba, ko sabanin siyasa ko kuma hassada wanda hakan kuma haramun ne."

- Sheikh Ishaq Adam

Kara karanta wannan

Yayin da ake rade radin tuge shi, Sultan ya tura sako ga rundunar sojoji

"Addu'a ya kamata a yi"- Malamin Musulunci

Sheikh Ishaq ya ce abin da ya kamata mu yi shi ne yi mata addu'a Allah ya kubutar da ita lafiya ba tare da matsala ba.

Sannan ya yi addu'ar Allah ya ci gaba da kare mu daga irin wannan iftila'i da sauran jama'a baki daya.

Ƴan bindiga sun sace mahaifiyar Rarara

Kun ji cewa wasu yan bindiga sun shiga kauyen Kajuru a jihar Katsina inda suka sace mahaifiyar mawaki, Dauda Kahutu Rarara.

Lamarin ya faru da tsakar dare a kauyen da ke karamar hukuma Danja a jihar inda ƴan sanda suka ce sun cafke mutane biyu da ake zargi da hannu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.