"Kul Fa": Cibiyar Shari'ar Musulunci Ta Yi Gargadi Mai Tsauri Kan Taɓa Kimar Sultan
- Yayin da ake ci gaba da dambarwa kan taba ikon Sarkin Musulmi, an gargadi gwamnatin Sokoto kan shigar da siyasa
- Cibiyar dabbaka shari'ar Musulunci ta gargadi gwamnatin jihar kan wasa da iko da kuma darajar da Sultan ke da shi a Najeriya
- Hakan ya biyo bayan zargin rage ikon Sultan bayan kirkirar sabuwar doka da Majalisar jihar ta yi wanda jama'a da dama suka kushe
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Sokoto - Cibiyar dabbaka shari'ar Musulunci ta gargadi gwamnatin jihar Sokoto kan wasa da rawanin Sarkin Musulmi.
Cibiyar ta tura gargadin ne yayin da ake zargin Majalisar jihar ta tabbatar da wata doka da zata rage ikon Sultan kan nadin hakimai.
Sultan: An gargadi gwamnatin Sokoto
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban cibiyar, Aliyu Ibrahim Altukri ya fitar, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Altukri ya ce suna daga cikin masu ruwa da tsaki a Majalisar Sultan inda suka ja kunnen gwamnatin kan saka siyasa a lamarin.
Cibiyar ta ce Sultan ba wata hukuma ba ce a cikin gwamnatin Sokoto illa wani mukami ne mai daraja da Musulman Najeriya ke mutuntawa, Daily Post ta tattaro.
"Muna daga cikin masu ruwa da tsaki a Majalisar Sultan kuma muna Allah wadai da wani yunkuri na shigar da siyasa kan lamarin."
- Ibrahim Alkutri
Dokar rage ikon Sultan kan nadin hakimai
Wannan na zuwa ne yayin da Majalisar jihar ta kirkiri wata doka kan nadin hakimai a jihar.
A baya, Majalisar Sultan na da ikon nada hakimai ba tare da sanin gwamnatin jihar ba amma wannan doka ta sauya tsarin.
A yanzu, Majalisar Sultan ba ta da ikon nadin hakimai ba tare da sahalewar gwamnatin jihar ba.
Sokoto: Kotu ta haramta dokar tsige hakimai
Kun ji cewa A zaman Majalisar jihar Sokoto na ranar Talata, an ruwaito cewa kudurin da zai yi gyara ga dokar masarautar ya tsallake karatu na farko da na biyu.
A sabuwar dokar za ta rage karfin ikon Mai alfarma Sa'ad Abubakar III, wanda ya haɗa da cire ikon naɗa hakimai ko masu naɗin sarki ba tare da izinin gwamnatin ba.
Asali: Legit.ng