Hotonan Yadda Aka Gudanar da Liyafar Murnan Dawowar Sarki Sanusi II a Kano
- Yayin da Gwamna Abba Kabri ya mayar da Muhammdu Sanusi II kujerar sarauta, wasu kungiyoyi sun nuna farin ciki
- Kungiyoyin da suka yi liyafar sun hada da kungiyar Muhammadu Sanusi II colloquium da 'Yan Dangwalen jihar Kano
- Kungiyoyin sun bada gudnmawa sosai wurin kiran Gwamna Abba Kabir ya dawo da Sanusi II bayan hawa mulkin jihar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Wasu magoya bayan Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II sun gudanar da liyafa ta musamman a jihar.
'Yan a mutun Sarkin sun taru ne domin nuna jin dadinsu bayan mayar da Sanusi II kan kujerar sarautar jihar.
Sanusi II: An gudanar da liyafar murna
Magoya bayan sun hada da kungiyar Muhammadu Sanusi II colloquium da 'Yan Dangwalen jihar Kano, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyoyin na daga cikin wadanda suka yi ta kiran mayar da Sanusi II kan kujerar tun bayan nasarar Gwamna Abba Kabir.
Ganawar ta musamman an yi ne domin nuna jin dadi da kuma godiya ga Allah game da dawowar Muhammadu Sanusi II.
Shugaban liyafar, Ibrahim Musa Abubakar da aka fi sani da Sanyi-Sanyi ya ce musabbabin taruwar shi ne taya Sanusi II murna.
"Ba za mu iya nuna jin dadinmu kan wannan lamari na dawo da Sanusi II kujerar sarautar jihar Kano ba."
"Wannan shi ne dalilin haduwarmu a yau domin yin godiya ga ubangiji da kuma murnan abin da ya faru a Kano."
- Cewar Sanyi-sanyi
Liyafar ta samu halartar manyan mutane da mukarraban gwamnati da sauran al'umma magoya bayan Sanusi II.
Kalli wasu daga cikin hotunan liyafar:
Sanusi II ya ba dattijo kyautar N200,000
A wani labarin, kun ji cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya taimakawa wani dattijo bayan ya nemi taimako kan iftila'i a gidansa.
Dattijon ya bukaci taimako ne bayan wani bangare na gidansa ya rushe saboda mamakon ruwan sama da aka yi a jihar Kano.
Sanusi II ya gwangwaje dattijon da kyautar har N200,000 domin ya yi amfani da shi wurin gyaran bangaren da ya rushe.
Asali: Legit.ng