Borno: Mutane Sun Mutu Bayan Wata Ta Kai Harin Bam Kan Masu Zaman Makoki

Borno: Mutane Sun Mutu Bayan Wata Ta Kai Harin Bam Kan Masu Zaman Makoki

  • Wata 'yar kunan bakin wake ta tayar da bam yayin da ake zaman makoki a karamar hukumar Gwoza da ke jihar Borno
  • Lamarin ya faru ne a yau Asabar 29 ga watan Yunin 2024 inda aka tabbatar mutane shida sun rasa rayukansu
  • Wannan na zuwa ne bayan wani hari kan masu bikin aure da ya yi sanadin hallakar wasu mutane da dama a jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Borno - Akalla mutane shida ne suka rasa rayukansu bayan kunar bakin wake kan masu zaman makoki a jihar Borno.

Lamarin ya faru ne a yau Asabar 29 ga watan Yunin 2027 a karamar hukumar Gwoza.

'Yar kunan bakin wake ta hallaka mutane a zaman makoki
An rasa rayuka da dama bayan harin bam a jihar Borno.
Asali: Original

Borno: Bam ya hallaka masu zaman makoki

Kara karanta wannan

‘Yar kunar bakin wake ta dasa bam a Borno, mutane sun mutu a wajen biki

Zagazola Makama ta tattaro cewa harin ya faru ne kusa tashar mota mai cunkoso da aka fi sani da Marrarraban Gwoza.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan 'yan sanda a jihar, Yusuf Lawal ya tabbtar da faruwar lamarin inda ya ce mace ce ta tayar da bam din.

Lawal ya ce akalla an samu mutane 15 da suka samu raunuka bayan mutuwar mutane shida tun farko, cewar Punch.

Wani shaidan gani da ido mai suna Buba ya ce wacce ta kai harin ta yi kokarin tayar da bam din ne kan masu gudanar da bikin aure.

An sanya dokar hana fita a Gwoza

Daga bisani an sanya dokar hana fita a Gwoza saboda kokarin dakile faruwar irin haka ko wata barazanar tsaro.

Wannan hari ne kunan bakin wake na zuwa bayan samun sauki a hari makamancinsa a jihar na tsawon lokaci.

Kara karanta wannan

Kano: Ana fargabar mutane sun mutu yayin da gini ya rufta kansu ana ruwan sama

Jihar Borno ta sha fama da hare-haren Boka Haram tun shekarar 2009 wanda aka shafe shekaru ana gwabzawa da su.

Boko Haram sun sace babban alkali

A wani labarin, kun ji cewa 'yan ta'addar Boko Haram sun sace daya daga cikin manyan alkalan babbar kotun jihar Borno.

Rahotanni sun yi nuni da cewa alkalin mai suna Haruna Mshelia ya hadu da ƴan ta'addar ne yayin da yake tafiya a kan hanya.

An tabbatar da cewa yan Boko Haram sun fito ne daga daji suka tsaya kan hanya yayin da alkalin ke kokarin wucewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.