Kungiyar Musulmi Ta Yi Ƙarar Sarkin Ogbomoso, Kotu Ta Haramta Tsige Limamin Juma’a
- Babbar kotun jiha ta haramta basarake da 'yan majalisar masarautarsa daga tsige babban limamin Ogbomoso
- Mai shari'a K.B. Olawoyin ya kwaɓi sarkin Ogbomoso, Oba Afolabi Ghandi daga tuɓe rawanin Sheikh Teliat Yunus
- Wannan na zuwa ne bayan da masarautar Ogbomoso ta zargi Sheikh Teliat da zuwa aikin Hajji ba tare da izini ba
Jihar Oyo - Babbar kotun jihar Oyo da ke Ogbomoso ya dakatar da masarautar Ogbomoso, daga tuɓe rawanin babban limamin Ogbomoso, Sheikh Teliat Yunus Ayilara.
Mai shari'a K.B Olawoyin ya kwaɓi sarkin Ogbomoso, Oba Afolabi Ghandi Olaoye da masu naɗin iyayen sarki daga taɓa rawanin Sheikh Teliat.
Kotu ta hana sarki ya tsige babban limami
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa kungiyar Musulmi ta RTOMYF ne suka yi ƙarar sarkin da 'yan majalisarsa bayan yunkurin tsige limamin da aka yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Karar mai lamba HOG/31/2024, na da kungiyar Musulman a matsayin masu shigar da kara, da kuma sarkin Ogbomoso da 'yan majalisarsa matsayin wadanda ake ƙara.
Mai shari'a Olawoyin ya takawa basaraken da majalisarsa burki daga taɓa rawanin babban limamin.
Me ya jawo za a tsige Sheikh Teliat?
A ranar Alhamis ne muka ruwaito cewa sarkin Ogbomoso, Oba Afolabi ya yi yunkurin tsige Sheikh Teliat saboda ya je aikin Hajji ba tare izinin masarautar ba.
An ce Sarki Afolabi ya zargi Sheikh Teliat da saɓa dokokin da aka shinfida masa kafin a bashi muƙamin babban limamin.
Basaraken a cikin takardar zargin da ya aikawa Sheikh Teliat ya ce limamin bai nemi izni ba kafin wucewa aikin Hajji a Saudiyya, wanke ke nufin ya yi gaban kansa.
Rahotanni sun bayyana cewa an daɗe ana takun saka tsakanin basaraken da limamin, inda wannan karon allura ta kusa tono garma.
"Har yanzu Sanusi II sarki" - NNPP
A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyar NNPP ta dage kan cewa har yanzu Muhammadu Sanusi II shi ne halastaccen sarkin Kano.
Jam'iyyar ta ce hukuncin da babbar kotun tarayya da ke a Kano ta yanke kan rikicin sarautar bai sauya komai daga matsayin Sarki Sanusi II ba.
Asali: Legit.ng