Tsohon Sanata Ya Ji Ana Yunkurin Gina Asibiti a Majalisa, Ya Tona Asirin Masu Mulkin Najeriya
- Kashe kudi domin a ginawa ‘yan majalisar tarayya asibiti na a-zo-a gani ya samu suka tun daga wajen ‘yan siyasa
- A wajen Shehu Sani, facaka da dukiyar talakawa za a yi idan aka ce za a ginawa ‘yan majalisa wani katafaren asibiti
- Sanata Sani ya bayyana cewa ko a yanzu akwai karamin asibitin da babu ruwan ‘yan majalisa da sanatoci da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Shehu Sani bai jin tsoron fadan gaskiya a ko ina ne, saboda haka ne ya yi suna wajen yabo maganganu a dandalin sada zumunta.
Wannan karo Shehu Sani ya soki tsofaffin abokan aikinsa da ke majalisar tarayya a kan yunkurin gina katafaren asibiti a birnin Abuja.
Gina asibitin 'yan majalisar tarayya a Abuja
A ranar Juma’a da kimanin karfe 6:30 na yamma, Sanata Shehu Sani ya yi magana game da zancen ginawa ‘yan majalisar tarayya asibiti.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘Dan siyasar bai ganin akwai bukatar hakan, asali ma yana ganin asarar kudin jama’a ne lokacin da ake kuka da albashin 'yan majalisar.
Kamar yadda ya bayyana a shafinsa na X wanda mutane su ka fi sani da Twitter, asarar kudi ne a kashe tulin dukiya wajen gina wannan asibiti.
Ashe 'yan majalisa suna da karamin asibiti?
Dalilin tsohon Sanatan na Kaduna ta tsakiya shi ne yanzu haka akwai dakin shan magani a majalisar tarayyar da ke babban birnin Abuja.
A nan ne Sanatan ya yi bayanin abin da mafi yawan jama’a ba su sani ba, ya ce duk da akwai dakin shan maganin, sam ba a amfani da shi.
Shehu Sani ya ce da wahala ake samun wani Sanata ko ‘dan majalisar wakilai ya yi amfani da dakin shan maganin da ke majalisar tarayyar.
Matsayar Shehu Sani kan asibitin majalisa
"Gina sabon asibiti domin Sanatoci da ‘yan majalisar wakilan tarayya asarar dukiyar al’umma ne kurum;"
"Ganin cewa akwai wani dakin shan maganin da aka tanada domin wannan aiki wanda yawanci ‘yan majalisa ba su amfani da shi."
- Shehu Sani
Sanata Shehu Sani ya yabi gwamnatin tarayya
Can da ya motsa kuma, sai aka ji Shehu Sani ya na cewa an manta da zancen karin mafi karancin albashin da za a yiwa ma’aikata.
Duk da wannan suka kuma, ‘dan siyasar ya yabi gwamnatin tarayya da ya ji an cire haraji a kan magungunan da ake shigowa da su Najeriya.
Majalisa za ta yarda a sayo jirgin sama
Najeriya na shirye-shiryen sayo jirgin wani balarabe da bashin banki ya tilasta aka raba shi da dukiyarsa kamar yadda aka samu rahoto.
Idan har Bola Tinubu ya nemi sayen jirgin sama daga ketare, Godswill Akpabio ya ce sun shirya mara masa baya a majalisar tarayyar kasar.
Asali: Legit.ng