ASUU: Malamai Rututu Masu PhD Sun Tsere daga Jami’a, An Bar Dalibai a Matsala a Bauchi
- Kungiyar ASUU ta bayyana cewa abubuwa ba su tafiya masu yadda ya kamata a jami’ar Sa’adu Zungur da ke jihar Bauchi
- Shugaban kungiyar malaman jami’ar ya ce babu wani tsarin fansho ko makamancinsa da ma’aikaci zai iya mora nan gaba
- wani malami ya shaidawa Legit Hausa akwai bukatar gwamnan Bauchi ta duba halin da ma’aikata su ke ciki a jami’ar SAZU
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Bauchi - ASUU ta jawo hankalin jama’a game da abubuwan da su ke faruwa a jami’ar Sa’adu Zungur (SAZU) da ke garin Bauchi.
Kungiyar malaman jami’a da aka fi sani da ASUU ta bayyana cewa jami’ar jihar Bauchi ta na fuskantar wasu manyan matsaloli.
Shugaban ASUU a Jami'ar Bauchi ya koka
Shugaban ASUU na reshen SAZU, Kwamred Auwal Hussain ya ce malaman jami’ar da yawa sun tsere a cewar Wikki Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Auwal Hussain ya ce a jami’ar jihar Bauchi, babu tsarin fansho bayan an yi ritaya da sauran tanadi da ake yi domin ma’aikata.
Malamai sun bar jami'ar SAZU a Bauchi
Kungiyar ASUU ta ce a sakamakon haka malamai da-dama sun bar aiki a jami’ar SAZU don haka ake jan hankalin gwamnati.
Abin takaicin kamar yadda ya fada shi ne, fiye da malamai 20 wadanda sun yi digiri har zuwa na uku watau PhD sun bar makarantar.
Hussaini ya ce malaman da suka ajiye aikin sun cigaba da koyarwa da bincike a sauran makarantun da ma’aikaci zai mori aiki.
Shekaru 13 da kafuwa, ASUU ta ce har yau babu tsarin biyan hakkoki ga ma’aikatan da suka ritaya ko iyalan wadanda suka mutu.
Abin bai tsaya nan ba, duk karin albashi da kyautan da gwamnati ta ke ba ma’aikata saboda cire tallafin man fetur, bai kai gare su ba.
Yadda za a magance matsalolin jami'ar SAZU
Abdullahi Mustapha malami ne a jami’ar, ya shaidawa Legit Hausa akwai bukatar gwamnatin Bauchi ta saki kudi domin kula da jami’ar.
Wani bangare da ake kuka a jami’ar shi ne karancin gidajen ma’aikata musamman ganin yadda ake wahalar samun gidajen haya a Gadau.
Idan ma’aikata ba za su iya zama da iyalansu a kewayen jami’ar ba, malamin ya ce hakan zai kawo nakasa wajen karantar da dalibai.
Bayan haka, ana bukatar kwararru su shiga majalisar gudanar da SAZU tare da kokarin wajen inganta sha’anin malanta da karantarwa.
Ma'aikata sun gargadi gwamnati kan albashi
NLC ta ce zai zama kuskure babba idan aka bari gwamnoni suka yanke mafi ƙarancin albashi kamar yadda labari ya zo a karshen makon nan.
Kungiyar kwadago ta ce talauci mai tsanani zai iya bakuntar Najeriya idan haka ta faru don haka aka ja kunnen Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Legit.ng