Goodluck Jonathan Ya Kwantar da Hankalin 'Yan Najeriya Ana Cikin Tsadar Rayuwa

Goodluck Jonathan Ya Kwantar da Hankalin 'Yan Najeriya Ana Cikin Tsadar Rayuwa

  • Tsohon shugaban ƙasan Najeriya, Goodluck Jonathan ya yi magana kan ƙalubalen tattalin arziƙin da ƙasar nan ke fuskanta
  • Jonathan ya bayyana cewa nan ba da daɗewa ƙasar nan za ta shawo kan matsalar wacce ta addabi al'ummar ƙasar
  • Tsohon shugaban ƙasan wanda ya ce matsalar ta shafi kowane ɓangare ne ya nuna akwai buƙatar a haɗa ƙarfi da ƙarfe domin magance ta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bayelsa - Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya ce nan ba da daɗewa ba Najeriya za ta shawo kan ƙalubalen tattalin arziƙin da ke addabarta.

Goodluck Jonathan ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya na yin iyakacin ƙoƙarinta wajen ganin ta shawo kan matsalar.

Kara karanta wannan

An ba alkalai cin hanci a shari'ar zaben shugaban kasa na 2023? Gaskiya ta bayyana

Jonathan ya yi magana kan tattalin arzikin Najeriya
Goodluck Jonathan ya ce nan ba da dadewa ba Najeriya za ta magance matsalar tabarbarewar tattalin arziki Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Jonathan, wanda ya samu wakilcin basaraken ƙabilar Abureni a jihohin Bayelsa da Rivers, Collins Daniel, ya bayyana hakan a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa, a ranar Juma’a, cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An wakilci tsohon shugaban ƙasan ne a wajen taron ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa (NBA) reshen jihar Bayelsa, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Me Jonathan ya ce kan matsalar tattalin arziƙi?

"Bari na tunatar da mu cewa halin da ake ciki a halin yanzu na taɓarɓarewar tattalin arziƙin da ƙasar nan ke fama da shi bai taƙaita ga ɓangaren shari’a ba, domin ya shafi kowane ɓangare ne."
"Saboda haka muna buƙatar haɗa ƙarfi da ƙarfe domin nemo hanyoyin magance ta. Ƙalubalen zamantakewa ba baƙo ba ne ga ɗan Adam. Bayan yaƙin duniya na farko, duniya ta fuskanci matsalar taɓarɓarewar tattalin arziƙi a shekarun 1929/1930. Najeriya ba a bar ta a baya ba."

Kara karanta wannan

Majalisa ta fadi matakin dauka idan Tinubu ya bukaci a siyo masa jirgin sama

"Tsakanin shekarar 2016 zuwa 2019, duniya ta ƙara faɗawa cikin matsalar taɓarɓarewar tattalin arziƙi."
"Najeriya ta fuskanci na ta matsalolin na ƙuncin rayuwa, amma mun yi sa'ar ficewa cikin taɓarɓarewar tattalin arziƙin cikin ƴan shekaru kaɗan."

- Goodluck Jonathan

Kalaman Jonathan ga Buhari

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya gargaɗi Muhammadu Buhari lokacin da yake barin kujerar mulki a shekarar 2015.

Jonathan ya ce yana tausayin gwamnatin da za ta karɓi mulki a wancan lokacin inda ya nuna damuwa kan halin da za su tsinci ƙasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel