Ana Kukan Babu Kuɗi, Gwamnati Na Shirin Ginawa Ƴan Majalisun Tarayya Katafaren Asibiti

Ana Kukan Babu Kuɗi, Gwamnati Na Shirin Ginawa Ƴan Majalisun Tarayya Katafaren Asibiti

  • Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya bayyana cewa a wannan shekarar za a ginawa 'yan majalisar tarayya katafaren asibiti
  • Sanata Akpabio ya bayyana cewa sanatoci, 'yan majalisar wakilai, ma'aikata da baƙi ne za a riƙa dubawa a cikin asibitin idan an gina shi
  • Shugaban majalisar ya zayyana wasu kudurorin doka guda 25 da majalisar dattawan ta 10 ta amince da su a cikin shekararta ta farko

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya ce akwai shirin da ake yi na ginawa 'yan majalisar tarayya, ma'aikata da baƙin majalisar wani katafaren asibiti.

Sanata Akpabio ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Abuja yayin gabatar da jawabin maraba da dawowa zaman majalisar dattawa bayan hutun babbar Sallah.

Kara karanta wannan

Shigar banza: An kori mataimakiyar shugaban masu rinjaye daga zauren majalisar Edo

Majalisar dattawa ta yi magana kan gina asibiti
Za a gina katafaren asibiti domin amfanin 'yan majalisar tarayya. Hoto: @NGRSenate
Asali: Facebook

Majalisa za ta gina katafaren asibiti

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa majalisar tarayyar ta 10 wadda ta cika shekara 1 a ranar 13 ga watan Yunin 2024 tana da cibiyar kiwon lafiya da yanzu take aiki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Akpabio ya ce idan aka kamma ginin asibitin zai zama cibiyar kula da lafiyar 'yan majalisar dattawa, wakilai, da sauran ma'aikatan majalisun biyu.

Shugaban majalisar ya ce:

"A wannan shekara ta biyu, muna da shirin gina asibiti na zamani wanda zai zama cibiyar kula da lafiyar sanatoci, 'yan majalisun wakilai, ma'aikatan majalisar tarayya da baƙin mu."

Majalisar dattawa ta amince da dokoki 25

Sanata Akpabio ya zayyana wasu kudurorin doka guda 25 da majalisar dattawan ta 10 ta amince da su a cikin shekararta ta farko, in ji rahoton The Punch.

Daga cikin kudurorin akwai kudurorin dokar hukumar bunkasa Kudu maso Gabas, dokar bunkasa Arewa, sauya taken Najeriya da hukuncin kisa ga masu safarar kwayoyi.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa ta yiwa Tinubu gata, an tsawaita wa'adin aiwatar da kasafin 2023

Haka zalika, shugaban majalisar dattawan ya ce sun amince da dokar karawa ma'aikatan shari'a albashi da dokar asusun tallafawa masu yi wa ƙasa hidima da dai sauran su.

Majalisar dattawa ta ƙara wa'adin kasafin 2023

A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar dattawa ta amince da bukatar Shugaba Bola Tinubu na kara wa'adin aiwatar da kasafin kudin 2024.

Majalisar ta amince kasafin 2023 zai ci gaba da gudana tare da kasafin 2024 har zuwa ƙarshen shekarar 2024, lamarin da ya jawo cece-kuce a zauren majalisar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel