Gwamnatin Tarayya ta Dauko Tallafi da Ayyukan Inganta Rayuwar 'Yan Kasa

Gwamnatin Tarayya ta Dauko Tallafi da Ayyukan Inganta Rayuwar 'Yan Kasa

  • Gwamnatin tarayya ta ware makudan kudi domin gudanar da ayyukan gine-gine da tallafawa 'yan kasa domin rage radadin rayuwa
  • Mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngalela ya bayyana cewa gwamnati za ta gina manyan tituna da layukan dogo
  • Daga cikin sauran ayyukan akwai ware makudan kudi wajen sayo kayan abinci da za a rabawa talakawan Najeriya da raba kudi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Gwamnatin tarayya ta bijiro da wasu manyan ayyuka da domin rage radadin da 'yan Najeriya ke ji.

Ayyukan na karkashin gagarumin aikin gine-ginen kasar nan da tallafawa jama'a da gwamnatin Bola Tinubu bijiro da shi.

Kara karanta wannan

Rikicin sarauta da shari’ar zabe ba su taka masa burki ba, an nada Abba gwarzon Gwamnoni

Bola Tinubu
Gwamnatin Tinubu ta bijiro da manyan ayyukan gine-gine Hoto: Ajuri Ngalale
Asali: Facebook

Mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa za a gudanar da ayyukan a dukkanin sassan Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Waɗanne ayyuka za a yi?

Babban mataimakin shugaban kasa kan hulda da jama'a, Frederick Nwabufo, ya wallafa jerin ayyuka takwas da za a gudanar karkashin shirin a shafinsa na X.

Jerin ayyukan da za a gudanar;

1. Gina babban titin Sokoto-Badagry wanda zai ratsa ta Sokoto, Kebbi, Niger, Kwara, Oyo, Ogun da Lagos.

2. Sauran ayyukan gina titunan musamman na babban titin Lagos-Calabar da ake yi a halin yanzu, da titin Trans-Sahara da zai hada ta Enugu, Abakaliki, Ogoja, Binuwai, Kogi, Nasarawa da Abuja.

3. Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da bayar da kason gwamnatin tarayya na kudin gina titin dogo na jirgin kasa da zai tashi daga Fatakwal-Maidugur da na tsagin Ibadan-Kano na layin dogon Lagos-Kano.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano ya ware N4.8bn domin gyara makarantu, mutane 17, 000 za su samu aiki

4. Za a gina titin Sokoto-Badagry saboda muhimmancinsa ga ci gaban ayyukan noma, musamman saboda jihohin da ke kewaye da shi.

5. An ware Naira Miliyan 10 domin rabawa ga jihohin kasar nan na sayo motoci masu amfani da sinadarin CNG da fara shirin amfani da su.

6. Rabon tallafin N50,000 ga gidaje 100,000 a jihohin kasar nan na tsawon watanni uku domin tallafa masu kan halin da kasa ke ciki.

7. Shirin ware wani abu ga kungiyoyin kwadago da sauran kungiyoyin farar hula da ke ayyukansu a kasar.

8. Ware N155bn domin sayo kayan abinci da za a raba da jama'ar tarayyar Najeriya.

Shugaba Tinubu ya aika da tallafi Kano

A wani labarin kun ji cewa gwamnatin tarayya ta kai daukin kayan masarufi da yawansu ya kai tan 2,706 domin rabawa ga mabukata.

Hukumar bayar da agajin gaggawa (NEMA) ce ta miƙa tallafin da ya hada da masara, dawa da gero ga Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.