NNPC Zai Karya Farashin Litar Fetur Zuwa N488 a Gidajen Man Najeriya? Gaskiya Ta Fito

NNPC Zai Karya Farashin Litar Fetur Zuwa N488 a Gidajen Man Najeriya? Gaskiya Ta Fito

  • Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) ya musanta ikirarin cewa ya yi sauye-sauye ga farashin man fetur a sassan kasar nan
  • Hakan ya biyo bayan wani rahoto da aka samu cewa NNPC ya amince da sabon farashin fetur zuwa N488 a kan kowace lita
  • Legit Hausa ta tuntuni manajan gidan wani mai a Kaduna wanda ya karyata sauke farashin tare da cewa yanzu haka lita tana kan N740

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) ya ƙaryata rahotannin da ke yawo a soshiyal midiya cewa ya zabtare farashin fetur.

Babban jami'in yada labarai na kamfanin NNPC, Olufemi Soneye ya bayyana cewa rahoton sabon farashin fetur "ƙanzon kurege ne."

Kara karanta wannan

IPMAN ta yi zama domin rage kudin litar mai, an bayyana sabon farashin da take bukata

NNPC yayi magana akan rage farashin man fetur
NNPC yayi magana akan daidaita farashin man fetur zuwa N488/lita. Hoto: @nnpclimited
Asali: Facebook

NNPCL ya karyata farashin man fetur

A zantawarsa da jaridar New Telegraph ta wayar tarho, Mista Soneye ya ce kamfanin NNPC zai fitar da sanarwa ne a hukumance idan ma an samu sauyin farashin fetur.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Soneye ya ce:

"Rahoton sabon farashin ƙanzon kurege ne. A hukumance za mu fitar da sanarwa idan har aka samu sauyin farashin mai."

Kamfanin NNPC ya sauke farashin litar fetur

A cewar wani rahoton "ƙarya" da ya mamaye intanet, NNPC ya umarci dukkanin 'yan kasuwar man Najeriya da su koma sayar da litar fetur kan N488 zuwa N557.

Rahoton ya kara da cewa:

"Umarnin ya fito daga NNPC a ranar Laraba, kuma an aika takardar umarnin ga manya, matsakaita da kananun 'yan kasuwar mai na kasar nan.
"Takardar umarnin ta nuna cewa za a rika sayar da litar fetur kan N557 a Maiduguri da Damataru, sai kuma N550 a sauran jihohin Arewa.

Kara karanta wannan

Jimillar bashin da ake bin Najeriya ya kai N121tr, an fadi dalilin karuwarsa

"A kudancin kasar, za a rika sayar da litar man kan N520, N511, N500, amma ban da Uyo inda za a rika sayar da shi kan N515. Legas kuwa zai koma N488."

Nawa ne farashin litar fetur yanzu?

Bayan jin wannan labarin, mun tuntubi manajan wani gidan wani mai a Kaduna, Muhammadu Mubarak domin sanin farashin litar fetur din a yanzu,

Mubarak ya ce yanzu haka suna sayar da litar fetur kan N740 a gidan mansu, kuma batun cewa an karya farashin fetur din ba gaskiya ba ne.

NNPC ya dauki mataki kan wahalar fetur

A wani labarin, mun ruwaito cewa kamfanin NNPC ya ce ya dauki matakai da za su taimaka wajen kama masu boye mai wanda hakan ke jawo wahala da tsadar man.

A yayin da NNPC ya ce ya hada kai da jami'an tsaro domin aiwatar da hakan, ya kuma ba ta tabbacin cewa ya tanadi mai da zai ishi Najeriya da dogon lokaci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.