Rikicin Sarauta: “Babu Ruɗani a Kano, Sanusi II Ne Halastaccen Sarki,” Inji NNPP

Rikicin Sarauta: “Babu Ruɗani a Kano, Sanusi II Ne Halastaccen Sarki,” Inji NNPP

  • Jam'iyyar NNPP ta dage kan cewa har yanzu Muhammadu Sanusi II ne halastaccen sarkin Kano duk da hukuncin kotun tarayya
  • Kakakin NNPP, Ladipo Johnson ya ce babbar kotun tarayya ba ta da hurumin sauraron shari'ar saboda sarauta alfarma ce ba 'yanci ba
  • Mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya yi kira ga jama'a da su yi watsi da batun hukuncin kotun tarayya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Kakakin jam'iyyar NNPP, Ladipo Johnson, ya dage kan cewa babu rudani a game da rikicin shari'ar sarauta da ya mamaye jihar Kano.

Mista Ladipo Johnson ya ce har yanzu dai, Muhammadu Sanusi II shi ne halastaccen Kano, biyo bayan hukuncin babbar kotun tarayya a jihar.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke hukunci kan sanatan PDP da ake tuhuma da buga takardar NYSC ta bogi

Jam'iyyar NNPP ta yi magana kan rikicin sarautar Kano
Jam'iyyar NNPP da gwamnatin Kano sun dage cewa Sanusi II ne halastaccen sarki. Hoto: @masarautarkano
Asali: Twitter

"Sanusi II ne halastaccen Sarkin Kano" - NNPP

Jaridar The Guardian ta ruwaito Mista Ladipo ya ce hukuncin da babbar kotun tarayyar ta yanke ba shi da tasiri saboda ba ta da hurumin sauraron shari'ar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Sarauta ba wai 'yanci ba ne, alfarma ce, don haka babbar kotun tarayya ba ta da hurumin a tsoma baki a lamarin jiha, don haka, Sanusi II ne sarkin Kano, babu jayayya."

- A cewar kakakin NNPP.

Ya kara da cewa lamuran da suka shafi sarautar jihar wani hurumi ne na gwamna.

'Dan siyasr ya ce kuma ko ba komai akwai umarnin babbar kotun jiha da ya haramta a tsige Mai martaba Muhammadu Sanusi II daga sarauta.

"Dalilin mayar da Sanusi II mulki" - Sanusi Dawakin Tofa

Shi ma da ya ke amsa tambayoyi, mai magana da yawun Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ce an mayar da Sanusi II kan mulki ne saboda dawo da martabar masarauta.

Kara karanta wannan

Sanusi II Vs Bayero: Manazarci ya hango makomar sarautar Kano bayan hukuncin kotu

Ya kara da cewa da a ce ba ayi wannan gyaran ba, to da kowanne gwamna idan ya hau mulki zai iya sauke sarki ya naɗa wanda yake so, inji jaridar Newscentral.

Ya dage kan cewa Sanusi II ne sahihin sarkin Kano yayin da yake kira ga jama'a da su yi watsi da hukuncin da babbar kotun tarayya ta yi.

An ba da umarnin fitar da Sanusi II

A wani labarin, mun ruwaito cewa babbar kotun tarayya da ke da zama a Kano ta ba da umarnin a fitar da Muhammadu Sanusi II daga fadar sarkin Kano.

Alkalin kotun, Mai shari'a S.A Amobeda ya ce ya ba da wannan umarnin ne domin tabbatar da adalci da zaman lafiya a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel