El Rufai Ya Karɓi Baƙuncin Kwankwaso Kwanaki Bayan Kai Wa Buhari Ziyara a Daura

El Rufai Ya Karɓi Baƙuncin Kwankwaso Kwanaki Bayan Kai Wa Buhari Ziyara a Daura

  • Jagoran jam'iyyar NNPP kuma jagoran ɗariƙar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyarar ban girma ga Nasir El-Rufai
  • Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa ya kai ziyarar ne a gidan tsohon gwamnan jihar Kaduna da ke garin Abuja domin su gaisa da juna
  • Wannan ziyarar dai ta jawo cece kuce a kafofin sada zumunta, inda har wasu ke alakanta hakan da shirin siyasa yayin da ake tunkarar 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya karbi bakuncin tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso a gidansa na Abuja.

Nasir El-Rufai ya karbi bakuncin jagoran jam'iyyar NNPP ne kwanaki kadan bayan ziyarar da ya kai wa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a Daura.

Kara karanta wannan

Zargin satar N432bn: El Rufai ya ɗauki matakin shari'a kan majalisar dokokin Kaduna

Kwankwaso ya yi magana kan ziyarar da ya kai wa El-Rufai
El-Rufai da Kwankwaso sun saka labule a Abuja. Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

Sanata Rabiu Kwankwaso ya wallafa a shafinsa na X a daren ranar 27 ga Yuni cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A yau na kai ziyarar ban girma ga tsohon abokin aiki na, H.E Nasir El-Rufai a gidansa na Abuja."

Kalli hotunan ziyarar a ƙasa:

Ziyarar Kwankwaso ga El-Rufai ta jawo magana

Jim kadan bayan kai wannan ziyarar, kafar soshiyal modiya ta dauki zafi, inda wasu ke alakanta ziyarar da wani shiri na siyasa.

Duk da cewa bai fito fili ya alakanta kalamansa ga ziyarar da Kwankwaso ya kai wa El-Rufai ba, amma tsohon hadimin Buhari, Bashir Ahmed ya ce:

"Da alama dai 2027 za ta riske mu nan kusa"

Kalli maganar a nan ƙasa:

Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Kano karkashin jam'iyyar PRP, Salihu Tanko Yakasai ya wallafa a shafinsa na X cewa:

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Abin da Sanusi II ya fadawa kungiyar mata masu tafsiri a fadarsa

"Ina fatan dai shugaban kasa na sane da abubuwan da ake shiryawa. Ba shakka, zai iya zama abin hari a 2027. Ka watsar da naka, wanda kake so na kokarin watsa ka."

El-Rufai, Kwankwaso: "Jagororin siyasar Arewa"

Ma'abota amfani da kafar X sun cika a shafin Sanata Kwankwaso bayan wallafa hotunan ziyarar da ya kai wa El-Rufai, da yawansu na cewa:

"Yan siyasa biyu mafi daraja a Arewa. Shiyyar mu na alfahari da ku.
"Ku ne kaɗai mafi nagartar 'yan siyasa da muke da su a Arewa.
"Ya zama wajibi Arewa ta jira na tsawon shekara takwas kafin sake karbar mulki. Ba lallai ne ace Tinubu za a zaba a 2027 ba, amma dole a bar Kudu ta karasa wa'adinta"

El-Rufai ya ziyarci shugaban jam'iyyar SDP

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon gwamnan Kaduna, El-Rufai ya ziyarci shugaban jam'iyyar SDP, Alhaji Shehu Gabam a ofishin jam'iyyar da ke Abuja.

Kara karanta wannan

"Kungiyar nadamar tarayya da Tinubu": ɗan PDP ya yi shaguɓe ga El-Rufai, Kwankwaso

Wannan ziyarar da El-Rufai ya kai ofishin SDP ya jawo surutu sosai a soshiyal midiya, musamman ganin cewa tsohon gwamnan ya rasa kujerar minista a gwamnatin Tinubu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel