Yajin Aiki: ASUU Ta Fadi Matakin da Ta Dauka Bayan Ganawarta da Gwamnatin Tarayya

Yajin Aiki: ASUU Ta Fadi Matakin da Ta Dauka Bayan Ganawarta da Gwamnatin Tarayya

  • Kungiyar malaman jami'o'in Najeriya (ASUU) ta ce tana kan duba yiwuwar janye kudirinta na tsunduma yajin aiki a faɗin ƙasar nan
  • Shugaban ƙungiyar, Farfesa Emmanuel Osodoke ya ce bayan ganawarsu da gwamnatin tarayya, sun tsahirta daga shiga yajin aikin
  • Sai dai Farfesa Osodoke ya ce babu abin da zai hana kungiyar ta dauki mataki ma damar gwamnatin Tinubu ba ta biya bukatunsu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaban ƙungiyar malaman jami'o'i (ASUU), Farfesa Emmanuel Osodoke ya ce kungiyar na duba yiwuwar janyewa daga kudirin shiga yajin aikin da suka yi niyya a baya.

Farfesa Osodoke ya ce sun fara duba batun ne bayan ganawarsu da jami'an gwamnatin tarayya karkashin jagorancin ministocin Ilimi, Farfesa Tahir Mamman da Dakta Tanko Sununu.

Kara karanta wannan

ASUU ta tsorata Gwamnatin Bola Tinubu, an fara zaman tattaunawa a Abuja

ASUU ta yi magana kan shiga yajin aiki
ASUU ta dauki matsaya kan shiga yajin aiki bayan ganawa da gwamnati. Hoto: @asuunews
Asali: Twitter

ASUU ta tsahirta daga shiga yajin aiki

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, Farfesa Osodoke ya ce a yanzu dai sun dakatar da batun shiga yakin aikin zuwa wani dan lokaci domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar shugaban kungiyar ASUU:

"Mun tattauna kan matsalolin da a baya mu ka gabatarwa gwamnatin, kuma mun samu amsoshi daga jami'an da gwamnatin ta turo.
"A yanzu dai za mu koma mu sanarwa mambobinta abin da muka tattauna a taron ta yadda za mu cimma matsaya kan mataki na gaba."

Kungiyar ASUU ta yi shirin ko-ta-kwana

Jaridar Vanguard ta ruwaito Farfesa Osodoke ya ci gaba da cewa:

"Shekara daya kenan da hawan Tinubu shugaban kasa amma ko sau daya ba a taba kiranmu wani taro ba. Yau ce ranar farko ta tattaunawarmu da gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi yunƙurin takaita babban limamin Musulmi a jihar Kaduna

"Akwai tsare-tsare da muka yi, kuma mun amince kan wani wa'adi. Za mu je mu tattauna kan matsalolin, idan har babu wani abin kirki daga gwamnati, za mu dauki mataki."

Farfesa Osodoke ya ce jami'an gwamnatin tarayya sun ce za su yi duk mai yiwuwa na ganin ASUU ba ta shiga yajin aikin ba wanda ka iya kawo tsaiko ga karatun jami'a.

Gwamnati za ta biya SSANU rabin albashi

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta yanke shawarar fara biyan rabin albashi ga ma'aikatan jami'o'i da aka rikewa albashi tun daga shekarar 2022

Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana hakan ga manema labarai inda yace an mika bukatar ga Shugaba Bola Tinubu wanda ake jiran amincewarsa domin biyan kudin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel